Bani Da Lafiya Kashi Na Tamanin Da Biyu (82)

0 539

“A duk inda kukaga masu hulda da bokaye za ku same su ba su da wata nutsuwa kullum a hargitse kuma a firgice kuma ko da yaushe su ne a kasa ba sa taba ci gaba, saboda sun kama ba daidai ba, sun saki reshe sun kama iska, sun saki ALLAH sun kama wanin ALLAH ai kam dole ne ayita ganin ba daidai ba. Matukar kuna so kuga dai-dai a rayuwarku ta duniya da lahira to ku saki KOWA ku kama ALLAH da hanyar MANZONSA (S.A.W) kawai .”

Labeeba ta hango Maman Sultan sai take nunawa Bareerah tana cewa: Yar uwa kinga mutuniyarki, Allah yasa dai ta saurari wannan muhadarar da aka gabatar a yau din nan ko Allah zai sa ta shiryu.

Bareerah: Anya kuwa, da kyar ne idan tana ciki muhadarar nan, domin banga wata alama ba kam.

Suka wuce ta gabanta sukayi mata sallama, amma Maman Sultan ko kallonsu batayi ba balle ta amsa sallamar su.

Bayan sun wuce ne sai Labeeba tace: Kingani ko, hatta ma kallo bamu isheta ba ko tab dijam, ai idan ta nice ko sallama ma bazamuyi mata ba yasin.

Bareerah: ALLAH sarki, ai yar uwa ko saboda nan gaba ba’ayin haka ga Musulmi, duk rashin kirkinsa, duk rashin mutuncinsa idan kun hadu kiyi masa sallama, ruwansa ne ya amsa ko karya amsa ke dai kinyi abinda yadace kuma kin samu lada, ta yiwu hakan wata rana ALLAH yaganar da shi cewa abinda yake bai kyautawa, kinga a sanadiyyar ki ALLAH ya sa ya shiryu.

Bayan an idar da Sallah dinne sai kowa yana sauri domin yakoma inda ake gabatar da muhadarar.

Su Labeeba ma suka fito sai suka hango Iyayensu su Ummu Labeeba da Ummu Bareerah a tsaye tare da Maman Sultan suna magana.

Kai tsaye kuma cikin sauri suka nufi wurin domin suga kuma suji abinda Maman Sultan ke fada musu, saboda a zatonsu ai basu san wacece Maman Sultan ba kuma basu san irin sharrin da take yadawa a tsakanin al’umma ba.

(Insha ALLAH a rubutu na gaba za muji abinda suke tattaunawa tsakanin Iyayen su Labeeba da Maman Sultan.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Domin karin bayani:

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »