Bani Da Lafiya Kashi Na Sabain Da Daya (71)

0 531

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

” Mu yawaita karanta Ayatul Kursiyyu da Surorin Falaqi da Nasi musmaman a lokacin da za mu kwanta bacci saboda neman Allah yakare mu daga sharrin Kambun-baka da na hassada, saboda tasirin sharrinsu a jikkunan mutane ya zarce wanda shafar jinnu ke haddasarwa, ga naci da qalata wajan son dauwama a jikin mutum da sanya cututtuka iri-iri. Allah ya kyauta.”

Malamin yace: Ai shi Kambun-baka galibi wanda yake da shi ma bai sanin yana da shi, amma ita hassada ba haka bane saboda zuciyar mai ita tana sane.

-Mai hassada hassadarsa tana iya yin tasiri ne akan mutumin da ake ganinsa ko wanda yake halarce a gurin da ma wanda ba a gani ba kinsa kuwa b aya wurin, amma shi Kambun-baka dole ne sai wanda ake gani ne kawai Kambun-bakan yake iya tasiri akansa.

-Tasirin Kambun-baka ya fi tasirin hassada tsanani a jikkunan mutane da ma dukiyoyinsu.

-Tasirin hassada yana iya tasiri ne akan abinda mutum yake jiran mallaka ( kamar ni’imar da mutun ke shirin mallakarta) da ma wanda ya mallaka, amma shi Kambun-baka yana yin tasiri ne kadai akan abinda mutum ya mallaka.

Mai kambun-baka lamarin sa zai iya tasiri ne a kansa, dukiyarsa da kuma iyalansa a duk lokacin da ya yabi wani abu a cikinsu sai kaga abin yana tabarbarewa… Sabanin mai hassada shi sai dai tayi tasiri ne akan wani ko wasu amma ba akan shi ko dukiyarsa ba.

Ita Hassada asalinta kyashi ne, mugunta ce, bakin ciki ne kuma mummunan fata ne, amma shi kambun-baka ba haka yake ba .

Lamarin Kambun baka yanzu ya zama ruwan dare saboda yana shafar mutane da dama wajan sanya rashin lafiyar da ba ta jin magani, yana shafar dukiyarsu ta yadda lamari zai ta dagulewa, ya shafi ma’aurata wajan haifar da rashin jituwa tsakanin su, ya shafi kasuwancin su, da kuma harkar karatun su ( da sai kaga mutum yana ganewa amma yanzu abubuwan duk sun rikice kuma kokarin dai yana nan bai yi sakaci ba) duk kaga lamari ya dagule gaba daya.

Mai gabatarwa yace : Alhamdulillah Mallam ALLAH yasaka da Alkhairi, amma yanzu to menene mafita?

(Insha ALLAH a rubutu nagaba za muji ci gaban lamarin.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »