Malamin yace: To ka dai ji kadan kenan daga cikin abubuwan da suke sanya mutum ya zama yana da Kambun-baka har a rika ganin shi a matsayin maye saboda irin tasirinsu kusan daya ne.
Ummu Bareerah ta fuskanci Ummu Labeeba sai take cemata: Wato Ummu Labeeba fatan dai kinji bayanin nan ko? Ai shiyasa nake sanar da yarana cewa:Su saba da fadin “BARAKALLAH MAASHA ALLAH” a duk lokacin da sukaga wani abinda ya burge su ko da kuwa girki sukayi ya burgesu to su fadi haka ko suce: “MAASHA ALLAH” ya fi wannan kalaman da suke fadi na rashin ma’ana.
Ummu Labeeba: Ai nima a baya ba na fadin wanna Addu’ar, sai lokacin da naje yiwa wata mata barkar haihuwa naji wata Malama tana yiwa wata nasiha akan haka, na tambayeta sai tace min ai babu kyau yin haka ga abinda ake fadi nan, saboda idan Shedanu suka aro bakin mutum sai a yiwa mutum kazafin yana da Maita.
Abu Bareerah ya waiga yake cewa Ummu Bareerah: Fatan dai kina ji kuma kina rike bayanin da malamin nan yakeyi ko?
Ummu Bareerah: Kwarai kuwa ai har ma recording din Muhadarar nake yi kuma ina rubuta wasu muhimman jumlolin da yake fadi a cikin wannan takardar da ke hannuna, saboda wannan makobciyar mu din nan tana da bukatar idna nakoma nayi mata wannan bayanan saboda na fahimci kamar tana da Kambun-baka amma ita bata ma san tana da shi ba.
Su Bareerah da Labeeba suna gefe sai Labeeba take cewa: Wato yar uwa lamarin Kambun-baka din nan wallahy abin yana bani tsoro matuka, saboda ya wahalar da ni sosai fiye da yadda kowa zaiyi tsammani.
Bareerah: Ai haka suke dama, saboda suna da wuyar sha’ani ne ga nacin tsiya da zarar mutum ya warke sai kiga ya kara shiga wata matsalar.
Mai gabatarwa yaci gaba da tambayar malamin yana cewa: Shin mallam ya ake gane Bambanci tsakanin hassada ne da kuma Kambun-baka saboda munji kamar ka ce suna kamancece niya da juna a wani fanni.?
(Insha ALLAH za muji amsar bayanin a rubutu nagaba.)
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.
Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.
(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)
Domin Ƙarin Bayani Game Da Darrusan Marubucin.
+2348031542026
https://t.me/Rismawymedicine
rismawy86@gmail.com