Bani Da Lafiya Kashi Na Sabain Da Shida (76)

0 422

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Bani Da Lafiya

Malamar tace: Tabbas kuwa matukar mutum yana so Allah ya tsare masa jaririnsa tun kafin a same shi to ya rika yin wanna tsarin da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya koyar da mu shi ne : Karanta Addu’ar nan a lokacin da zai kusanci matarsa.

Malamar taci gaba da cewa: Kuma Addu’ar ba wata mai wuya bace kowa ma zai iya haddace ta, ga ta nan kamar haka:

“بسم الله، اللهم جنبنا الشيطان, وجنب الشيطان ما رزقتنا”

BISMILLAH, ALLAHUMMA JANNABNASH SHAITĀNA WA JANNIBISH SHAIDĀNA MĀ RAZAQTANĀ.”

Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya ce duk wanda ya karanta ta wannan Addu’ar a lokacin da zai kusanci matarsa kuma aka samu rabo a wannan daren to Shaidan bazai iya cutar da abinda aka samu ba. ( Kamar yadda yazo a cikin Hadisin Abdullahi Ibn Abbas wanda Imam Bukhari da waninsa suka rawaito shi).

Mai gabatarwa yayi tambaya yana cewa: Shin Malama wannan cutarwar da akayi maganar cewa: “Shaidan bazai cutar da shi ba” ana nufin cutarwa a Addininsa (wajan sanya shi rashin bin dokokin Allah yadda yakamata) ko kuwa cutarwa a jikinsa (wajan sanya masa cututtuka da sauransu) ?

Malamar ta amsa da cewa: Ai Annabi bai bayyana wace irin cutarwa bace cikin biyun nan, saboda haka za mu iya daukar duk guda biyun, cutarwa a Addini ko kuma a jikinsa ( Kamar yadda malamai sukayi bayani wajan fassarar hadisin), Allahu A’alam.

Mai gabatarwa : Maasha ALLAH, Malama Allah yasaka da mafificin AlkhairinSA duniya da lahira Ameen.

Malama: Ameen ya Rabb, tare da ku gaba dayanmu.

Wata mata tayi tambaya tana cewa: Shin Malama Idan ni na iya kuma na haddace wannan Addu’ar amma mijina bai iya ba, shin zan iya karantawa ni kadai ta wadatar da mu ko kuwa?

(Insha ALLAH a rubutu nagaba za muji amsar da za a baiwa matar)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Domin karin bayani:

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »