” Yawaitar samun hatsarurruka a abin hawa, yawan samun gobara a gidaje, karayar Arziki komai kataba ba labari ( bayan kuma a baya ba haka bane), rushewar kasuwanci, afkuwar wasu cututtukan da za a rasa gane kansu wannan wasu ne daga cikin ababen da Kambun-baka ke iya haddasawa a karshe kuma yakan iya kai mutum har cikin qabari (yana kisa), Saboda haka ya zama wajibi mu nemi tsarin ALLAH daga sharrin Kambun-baka.”
Malamin yace: Ai wato shi Kambun-baka wasu za kaga suna da Kambun-bakan ko Kambun-Ido ta yadda za su rika ganin wani abu su yabeshi sai kaga abin nan ya lalace, ko su kalleshi ma kawai sai kaga abin ya lalace, amma su basu ma san suna da kambun bakan ba.
Saboda rashin sanin ma sai kaga ko a jikinsa ne yaga wani abinda ya burge shi yana yabon abin nan kuwa sai ya lalace, ko kaga gonarsa ta kone, ko iyalansa sai dai kawai aga yaro yana ta rashin lafiya iri-iri yana ramewa, ko matarsa sai dai ayita ganin rashin jituwa atskaninsu, ko dukiyarsa sai dai aga tana komawa baya da sauransu.
Malamin ya kara da cewa: To kunga irin wannan da zarar an fahimci wani yana da irin wannan abin yana yabon wani abin da ya burge shi sai dai aga abun yana lalacewa to ba makawa ya zama mai Kambun-baka.
Mai gabatarwa yakara tambayar malamin yana cewa: Mallam ALLAH yasaka da Alkhairi, amma shin akwai wani sakaci ne da mutum yake yi tayadda zai zama mai Kambun-baka ta yadda indai ya yabi wani abinda ya burge shi sai dai aga yana lalace ko kuwa akwai wata kungiya ce da mutum ke iya shigarta sai ya zama mai Kambun-baka?
Malamin yace: Ai shi kambun-baka ba shi da wata kungiya, Mayu ne kawai ke da irin wannan tsarin, amma kuma akwai dalilan da suke haddasa mutum yazama mai Kambun-baka kamar haka:
1- Sakaci ko rashin kiyaye Azkaar na safiya da maraice da kuma na bayan sallolin farilla musmaman ma karanta Ayatul Kursiyyu da Surorin falaqi da Nasi.
2- Rashin yin Addu’ar Allah ya sanya albarka a duk lokacin da yaga abin da ya burge shi kuma ya bashi sha’awa, maimakon yace: “Allah yayi masa/ta Albarka ko Allah yasanya albarka” sai dai kawai kaga an qundumo ashariya, ko dai wasu kalamai masu kama da hakan ko da kuwa zuciyarsa ba ta nufin sharri ga abin, ananne kuma Kambun-bakan ke samun damar shiga sai yayi tasiri ga shi wannan abin da aka yiwa wannan furucin.
3- Yawancin masu Kambun-baka ko hassada suna furta magana ne ta yabo ga wani abu tayadda zuciyarsu kuma ba hakan suke nufi ba, kuma abinda suka boye a zuciyar ne na mummunan abu yake tasiri shiyasa furta Alkhairi ga wani abu matukar dai Zuciyar ba haka take nufi ba, to fa babu wani tasiri ko amfanin da furucin zaiyi.
“”””Misali: Kin dora hotonki ko na yaranki a social media sai wani ko wata suce: Kai Amma kina da kyau kaza da kaza ko yaron nan yana da Kumari/yana da qiba/yana da kyau dss ba tare da sunyi Addu’ar sanya Albarka ba, kuma ke ma bakiyiwa yaran Addu’ar neman tsarin Allah daga sharrin irinsu ba. Sai dai kawai kiga yaronki yana ta ramewa ko wani ciwo ya kama ku duk ku tsotse ku motse ayita magani amma shiru ba labari a rasa me ke damunku.”””
(Insha ALLAH a rubutu nagaba za muji ci gaban)
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.
Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.
(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)
Domin karin bayani:
Domin Ƙarin Bayani Game Da Darrusan Marubucin.
+2348031542026
https://t.me/Rismawymedicine
rismawy86@gmail.com
Allah yayi Mana jagora ya tsare mu da kariyarsa,
Amin Thuma Amin