Bani Da Lafiya Kashi Na Sittin Da Hudu (64)

0 420

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

“Duk mara lafiyar da yayi Imanin cewa: ALLAH ne kadai ke iya saukar da cuta kuma shi kadai ne ke iya warkarwa, to hakika ya ci rabin maganin cutarsa.”

Sai can Maman Sultan ta hango matar tare da wasu mutane a zaune , kai tsaye ta nufi wurin cikin sauri. Tana karasowa wurin ne ba tare da ta duba ta ga wadanda ke wurin ba sai kawai ta kasa baki tace:

” Haba baiwar Allah ina kika shigene haka? Ina ta nemanki ga shi Malamin ma ya ce kar mu wuce mintuna 30 saboda zai shiga wasu sabgogin. Don Allah taso mu wuce kar mu makara.”

Matar dai tayi shiru ta kasa cewa komai sai kallon Labeeb da Bareerah kawai take yi.

Maman Sultan dai taji matar ba wata amsa daga gareta, sai ta fahimci lallaikam akwai wani abu a kasa, sai hankalinta ya sake juyowa domin fahimtar shin suwanene ma a zaune a wurin tukunna..!

Tana dubawa sai taga ai fuskar su Labeeba ce da Bareerah, hankalinta ya kasa kwanciya sai cewa tayi: Ke kuma meye hadinki da wadan nan mutanen marasa son ci-gaban mutane, kifayen rijiya wadanda basu san rayuwa ba sai tsabar iyayi da nuna su na Allah ne ?

Su Bareerah kuwa suka yi biris da ita kamar basu ma ji abinda take cewa ba, sai Labeeba take cewa matar: Yar uwa, ke dai kinji abinda muka fada miki kuma ba fadarmu bace fadin Farin Jakada ne Dan Abdullahi amincin Allah sukara tabbata agareshi da iyalansa da sahabbansa da wadansa suka bisu da kyautatawa har ranar sakamko, domin SHI ne wanda yayi hani game da zuwa wurin bokaye da yan duba da kuma yan bori har ya tabbatar da wanda yaje wurinsu kuma ya yarda da abinda suka fadi da cewa Ya Kafurta, wanda ma bai yarda ba sai ya yi kwana 40 yana Ibada Allah ba ya amsa.”

Maman Sultan dai hankalinta ya tashi, amma abinka da wanda suke yiwa shedan aiki sai tayi ta maza ta daure cikin karfin hali take cewa: Ai dama na san za a rina tunda naganki da wadan nan munafukan na san sun yaudareki za su hana ki kiyi rayuwa mai dadi tunda su sun kiyinta.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »