Bani Da Lafiya Kashi Na Sittin Da Uku (63)

0 19

Matar dai taji yadda su Labeeba suka ruguza duk wani abinda Maman Sultan ke kokarin jefata ciki na zuwa wurin wani BOKA da sunan neman maganin samun mijin Aure.

Bareerah takara dafa kafadar matar take cewa: Yar uwa, karki rika damun Kanki ko ki saba da zuwa wurin malamai a duk lokacin da wata damuwa ta sameki ko kika shiga wani yanayi, malamin kuwa ko da na kwarai ne, domin anan gaba idan har kika saba sai kiga shedan yana kara ingizaki zuwa wurin wasu bokayen. Allah ya kyauta.

Matar : Eh lallaikam na ji wannan bayanin kuma na godewa Allah wanda ya hada ni da ku a daidai wannan lokacin da na kusa afkawa ga hallaka. To amma fa yar uwa kinsan wani lokacin mutum ba ya iya samarwa kansa mafita shi kadai dole ne sai ya nemi mafita daga wurin wasu malaman.

Bareerah: Ai idan shawara ce ko kuma wani abin dabam kamar neman maganin wasu cututtukan da sauransu wannan za ki iya zuwa ga masana fannin ( Su ma wadanda basu sabawa Shari’ar Allah ba), amma wasu abubuwan dole ne daga ke sai Allah kawai ki dage da yin sallaolin dare, Istigfaari, salatin Amnabi, sadaqa, Addu’o’i ba dare ba rana da sauran Ayyukan da suke kara kusantar da bawa ga ubangijinsa.

Matar: Masha Allahu, Allah yasaka da alkhairi.

Ba jimawa sai ga Mamam Sultan nan ta dawo, ta duba inda tabar matar bata ganta ba sai ta shiga cikin laburarin da zummar ko ta shiga ciki ne, nan ma dai bata ganta ba, sai ta fito waje tana ta waige-waige tana cewa:

“To ita matar nan ko ina tayi ne kuwa haka, ga shi kuma na sanarwa Malamin cewa muna nan zuwa da ita?”

(Insha Allahu za muji ci gaban lamarin a rubutu nagaba.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »