Bani Da Lafiya Kashi Na Sittin Da Biyu (62)

0 839

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Bareerah: Ai ingaya miki gaba dayansu su ukun nan da duk wasu dangoginsu Allah ya haramta yin hulda da su, ya tsine musu kuma sakamakon su wutar jahannama da duk masu zuwa wurarensu matukar suka mutu basu tuba ba.

Labeeba: Allah ya kyauta kuma yakara tsare mana Imaninmu, ai hatta ma wanda yaje wurinsu bai yarda da abinda suka fada masa ba to sai ya yi kwana 40 yana Ibada Allah ba ya amsa, balle kuma ace ya aminta da abinda sukace masa ai shikenan kuma ya zama mushriki kuma Kafiri wanda ya bar musulunci. Ya zama wajibi ne ki kaurace musu da duk wani mai hulda da su kamar irin su Maman Sultan.

Matar hankalinta yatashi sai take tambayar Bareerah cikin wani irin yanayi tana cewa: To ni dai yanzu tayaya ne zan iya gane su saboda yanzu sun cakudu da na kwarai din, suna yin basaja basu cika fitowa da irin siffofin nan da kika lissafo su ba kai tsaye ?.

Bareerah : Ai wannan mai sauki ne yar uwa, domin duk wanda kikaje wurinsa yatambayeki sunan mahaifiyarki, mijinki ko kuma saurayinki, ko ya nemeki ki samo wani abu na jikin mutum ko tufafi kamar : Gashi, Underwear, handkerchief, dankwali, takalmi, jinin al’ada ko ruwan maniyyi da sauransu, to ba shakka wannan BOKA ne kuma ya haramta aje wurinsa.

Labeeba: Bugu da kari ma, duk wanda kikaje yace miki zai duba miki yaga ko da alkhairi a tattare da mijin da zaki aura, ko wani abun dabam ta hanyar bugun kasa ko mai mu’amila da taurari da sauransu, to ba makawa shi ma ya Haramta kije wurinsa.

“Yoo wai ma meyasa idan kun shiga damuwa ko rayuwa ta yi muku tsauri sai ku rika zuwa wajan wasu bokaye da yan duba suna wahalar da ku, a karshe kuma ku dauwama cikin nadama mara amfani. Alhalin Allah ne kadai wanda ake komawa gareSHI wanda babu sauran nadama ko da-na-sani.”

(Insha Allahu za muji ci gaban bayanin a rubutu nagaba.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »