“Komai da kasani da ma wanda baka sani ba duk na ALLAH ne, kuma ALLAH ne kadai ke da ikon yayi yadda yaga dama da su, zai iya baiwa wani kuma ya hana wani, ko kuma ya kwace daga hannun wani, duk ikonSA ne wannan babu mai iya ce masa don me !.”
Hausawa ma sun ce: “In dai kaga mutum ya bar wani hali to ka tabbata ba halinsa bane,” haka nan dai Maman Sultan har cikin taxi din ma ba shiru tayi ba sai tallata hajar bokayenta take tayi ga mutanen da suka manta Allah a matsayin mai iko akan komai, tana cewa dayar:
” Ai ke ingaya miki idan kikaga yadda tarin yan matan da suka jima basuyi aure ba wasu ma har sun fara fitar da rai da auren, amma malamin nan ya shiga ya fita saboda tsabar kwarewarsa a aikin duk sai da sukayi aure, ai ingaya miki yanzu babu wacce take a waje duk suna gidan mazajensu.”
Zuciyar matar ta fara amincewa da zancen Maman Sultan, amma sai ta tambaya tana cewa: Nima fa kinga akwai wata yar uwata wallahy ta jima batayi aure ba, samarin sunki tsayawa kowa yazo sau daya to ba zai kara dawowa ba abin na damun mu sosai wallahi, munyi magungunan har mun gaji. Kina ganin za a iya samun mafita kuwa a wurinsa?
Maman Sultan: Ikon Allah, yoo shi wannan ai aikinsa kamar yankan wuka ne, babu abinda bazai iya yi ba.
Direban taxi din yaga dai ba zai iya yin shiru ba ganin yadda Maman Sultan ke neman hallakar da matar nan, sai yakada baki yake cewa: Wai Hajiya shin wannan mutumin malami ne shi ko dai boka ne?
Maman Sultan : Ikon Allah ku fa wallahi matsalata da irin ku kenan, da zarar kunga abu sai ku kama cewa wai wani boka ne menene da menene tswww.
Direban yayi murmushi sai yace: To ai Hajiya ni dai fa tambaya nayi nace: Boka ne shi ko malami? Don sau da yawa wallahi ana sanyawa bokaye sunan malamai kawai saboda a batar da batattu kuma wallahi galiban mata ne ke da wannan matsalar, kuma na ga yadda kuke tsaro tsarin wannan mutumin ba malamin kirki bane Boka ne kawai kai tsaye, kuma ai Addininmu ya yi mana hani da yin mu’amala da bokaye.
(Insha ALLAHu za muji ci gaban bayanin a rubutu nagaba.)
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.
Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.
(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)