Bani Da Lafiya Kashi Na Hamsin Da Shida (56)

0 548

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Direba: Kwarai kuwa yar uwa, ai dama tsintacciyar mage ba ta mage, kuma a maimakon wasu su rika daukar izina a irin mummunan karshe da sauran abubuwan da ke faruwa ga masu zuwa wurin bokayen nan, amma sai dai ka tarar sai kara kutsawa cikin lamurran bokayen nan suke yi abinsu, yanzu lamarin sai dai fatan ALLAH ya kara shiryar da mu hanya madaidaiciya amma abin ya zama ruwan dare har wadanda ma ba kuma tsammani yanzu a alaqa da bokaye a boye kawai saboda biyan buƙatar duniya.

Labeeba: Subhanallah ! To ita matar wane mataki ne ta dauka akan Maman sultan tunda dai yanzu ta yi sanadin kashe mata aure?

Direba: Ai da farko ta yi niyyar daukar matakin kaita kara kotu, amma sai wata kawarta tace mata: Kinga ki rufawa kanki asiri ki kyale wannan maganar haka kiyita istigfaari da tuba izuwa ga ALLAH akan abinda kika aikata, kinga ya zamar miki izina kenan ko saboda nan gaba, amma kai karar nan da kike shirin yi kawai tonawa kanki asiri za ki kara yi duk wanda bai san dalilin sakinki ba ma sai ya sani a yanzu kinga kin bar abin kunya a gari kenan saboda babu mai kara ganinki da wani mutunci.

Labeeba: Kai jama’a Allah dai yakara tsare mana imaninmu, wato ana hallakar da jahilai wallahi.

Direba: Ai Hajiya ba jahilai kadai ba, wallahi yanzu har masu sanin ma aka ahankali, kinga dai wannan matar kar ma kice batayi karatu ba, domin har koyarwa a islamiyya ta tabayi, da karatun ta iya gwargwado, amma sai ta biyewa hudubar shedan a karshe kuma yakaita ya baro, yanzu ta rasa abinda take ciki wanda take muradi ma ya kufce mata ta koma laluben allurar makaho a cikin duhun dare.

Labeeba: Haasha liLLAH ! Wai mutane ina ilimin da suka sani ne yake zuwa haka ? Kinsan zuwa wajan bokaye babu kyau haramun ne amma sai kaga ana zuwa saboda kawai abin duniya kaicooo.. ALLAH yakara tsare mana imaninmu.

Akazo bakin kofar makaranta sai Labeeba ta sauka daga taxi din kuma ta sallami direban, kai tsaye sai ta shiga Makarantar.

Akan hanyarta ta zuwa aji ne sai su Maman Sultan suna tsaye a gefe daya sai daya matar tacewa Maman Sultan : Laa, kinga wannan munafukar da muka hadu da ita a taxi dazu ashe dai itama nan makarantar take.

Maman Sultan : Eh kwarai kuwa itace wallahi almura kawai, amma bari na bita duk inda ta shiga don na gano fuskarta, sannan na koya mata darasi ko don gaba ba za ta kara yiwa wani haka ba.

(Insha ALLAHu za muji yadda aka kare tsakanin su Maman Sultan da Labeeba a rubutu nagaba.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »