Bani Da Lafiya Kashi Na Hamsin Da Biyar (55)

0 536

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

“Babu abinda BOKA zai iya yi miki, shi ma bawan Allah ne kamar ki ko kuma ma ince kin fishi daraja a gurin Allah, a maimakon ya gyara ko ya kara miki jin dadin zaman gidan miji, sai dai yakara rushe miki jin dadi da zaman lafiyar da kike ciki a gidan mijinki a karshe kuma ki rasa samun jin dadi a duniyar, a lahira kuma azabar ALLAH na jiranki matukar baki tuba ba har kika mutu. Allah yakara tsare man imaninmu.”

Labeeba: Ai maganin irinsu kenan dama, ai kinga yanzu a gaba ba lallai ne ta kara yarda da irin wannan ba kuwa. Amma to ya suka kare ne ita da Maman Sultan din?

Direba: Ai waya ta bugawa Maman Sultan din ta nuna mata maganin fa ya yi sabanin abinda ta nema, Ita kuwa Maman Sultan sai ta kara cewa su koma wurin bokan gobe don suji bahasin lamarin.

Labeeba: Kuma wai ta kara amincewa sukara komawa wurin bokan ?

Direba: Kwarai kuwa, ai kam haka aka yi, a karshe dai bokan ya kara Umartar ta da ta sake samo abinda yace ta samo na mijin wanda za a hada maganin da shi, suka kara kalallameta da kalamansu na yaudara har ta amince za ta kara samowa din.

Labeeba: Subhanallah ! Lallaikam duk wanda ya kuskura ya biyewa bokaye da malaman tsubbu na tabbata za su zamar da shi tamkar Ball (kwallon kafa) wani ya buga shi ta kai, wani ya shura shi da kafa, ALLAH dai ya kyauta.

Bani da lafiya

Direba: To dai kinga yadda lamarin wannan matar ya kasance abin tausayi, saboda ta kashe kudi bila adadin kawai akan wai ba ta son mijinta ya karo mata kishiya, ga basussuka suka taru a kanta, ga shi kuma ta siyar da kayayyakin dakinta da na kitchen sai yan kadan, kuma duk su Maman Sultan ne da bokaye suka cinye su, a karshe kuma bukata bata biya ba, saboda asiri ne yatonu har mijin yasan abinda ake ciki.

Labeeba: Subhanallah ! Ai ka ji irin matsalar ko… Wannan ma ya zama izina ga sauran matan auren da suke da irin wannan tunanin, kina zamanzamanki lafiya da mijinki kawai wata kawarki ko wata shirmammiya tazo ta zuga ki kuje gidan boka ko malaman tsubbu a karshe dai ga irin abinda ke faruwa da su nan, ba su ga tsuntsu kuma ba su ga tarko, anyi jifar gafiyar Baidu.

(Insha ALLAHu za muji ci gaban bayanin a rubutu nagaba)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »