Bani Da Lafiya Kashi Na Hamsin Da Bakwai (57)

0 616

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

ABIN LURA

“Ya zama WAJIBI mu shiga cikin hayyacinmu sannan mu guji zuwa wurin bokayen kauye da na birni, domin kaso mai tsoka cikin wadanda aljanu ke wahalarwa akwai wadanda suka hadu da su a gidan bokaye sai kuma wadanda kaikayi ke komawa kansu. Allah ya kyauta.”

Labeeba ta karaso aji amma sai ta tarar Monitan ajin yana sanar da cewa: Malamin da ke da lecture a lokacin ya bayar da uzurinsa saboda haka ba zai samu damar zuwa ba sai dai haduwa ta gaba kuma insha Allahu.

Jin haka ne yasa nan take Labeeba ta nufi laburari domin tayi nazarin karatuttukanta da bincike-bincikenta kamar yadda ta saba yi.

Ita kuwa Maman Sultan tana ta binta a baya har sai da taga labeeba ta shiga laburarin tukuna sai Maman Sultan taji wayarta na ringing sai ta koma gefe domin ta daga wayar, ta dau kusan mintuna 2 a tsaye tana wayar ne sai ta cewa matar da suke tare: Don Allah jira ni anan wurin kafn nadawo, wani kira ne na gaggawa minti 30 kawai zanyi nadawo.

Matar kuwa ta samu wuri ta zauna, bayan mintuna 10 ne sai taga Labeeba ta fito daga laburarin, sai matar ta waiga baya tana cizon yatsanta tana magana kasa-kasa tana cewa: Wayyoo Allah ! Ga shi kuma Maman Sultan din bata dade da wucewa ba.

Sai ga Bareerah nan sun hadu da Labeeba a kan hanya, kowacce ta dage niqabinta bayan sun gaisa ne shine Bareerah take tambayar Labeeba tana cewa: Ina zaki ne haka yar uwa?

Labeeba: Wallahy daga laburari nake ne sai naga nazarin dai sai ahankali dole sai na rika shan shayin na’a na’a wana aka dafa su tare da yayan Habbatus saudah tukuna, saboda wani mai magani ne yace min suna da matukar amfani ga dalibai ko masu bincike-bincike da nazarce-nazarce.

Bareerah: Masha Allah, ai wancan mutumin ma yana siyarwa, ah to ai nima kam tare za mu tafi domin mu siyo wannan fa’idah ba zata wuceni ba insha ALLAH.

Matar dai sai ta kama mamakinsu, saboda shigar da sukayi ma ta burgeta gwanin sha’awa kuma ga shi suna magana ta hankali cikin ladabi, nutsuwa tare da girmama juna. Sai zuciyar matar ta shiga wani saqe-saqe kamar haka:

“Wai me yasa Maman sultan ta nuna rashin jin dadinta ne akan abinda matar nan da direban Suka fadi ne a cikin taxi ?”

(Insha Allahu za muji ci gaban bayanin a rubutu nagaba.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »