Labeeba: Ai Umma na san matar sosai kuma itace ma wacce nataba baki labarinta kwanakin baya, har kika ja kunne na akan nayi baya-baya da ita saboda tsaro.
Ummu Labeeba: Eh kwarai kuwa na tuna, ai kusantar irin mutanen nanne sai ahankali saboda kar wata rana suje sukai mutum su baro.
Abu Labeeba: Kaicoo ! Kuma wai na ji ance ma ita bazawara ce, to in banda toshewar basirar wasu mutanen tayaya bazawara za tazo ta bani maganin mallakar miji ko na haihuwa ko kuma na samun mijin Aure? Ai na tabbata ita ma kanta ta fi su bukatar irin maganin nan da take maganarsa.
Labeeba: Ai Abba sunanta da keke ji ana ta Maman Sultan itama kanta ba haihuwar take yi ba, kawai suna ne ta sanyawa kanta saboda tanason sunan amma babu wani Sultan a duniya, tana dai son haihuwar sosai kuma hakanne ma yafito da ita daga gidan mijinta wajan tsawon shekaru tana waje. Amma wai a haka take kai mutane wurin bokaye neman maganin mallakar miji da na haihuwa.
Allah wadaran naka ya lalace.
Abu Labeeba: Ikon Allah, kinga irin sakarcin wasu mutanen ko! Tayaya zan rika neman wani abu a hannun bayin Allah, abinda babu wanda zai iya bayar da shi sai Allah Ubangijin kowa da komai, Ai idan Kura na maganin zawo tayiwa kanta mana mugani indai gaskiya ne.
Ummu Labeeba: Ai Abu Labeeba idan Allah ya batar da mutum babu mai iya shiryar da shi sai ALLAH shi kadai.
Abu Labeeba: Tabbas kuwa wannan haka yake, ALLAH yakara shiryar da mu hanya madaidaiciya. Labeeba sai ki hanzarta ki tafi makarantar don kar ki makara, sannan kuma ki kiyaye abinda na fada miki.
Labeeba tayi sallama da iyayenta tayi addu’ar fita gida sai ta kama hanyar makarantar, akan hanyar ne sai ta hau Taxi ta tarar da su Maman Sultan a cikin taxi din , ita Labeeba ta gane su amma su ba lallai ne su gane Labeeba ba saboda tana sanye ne da Niqab a fuskar ta.
(Za muji abinda ya faru a cikin Taxi din a rubutu nagaba.)
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.
Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.
(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)
Domin Ƙarin Bayani Game Da Darrusan Marubucin.
+2348031542026
https://t.me/Rismawymedicine
rismawy86@gmail.com