Bani Da Lafiya Kashi Na Hamsin Da Hudu (54)

0 615

ABIN LURA

“Duk wacce kuka ga ta je wurin bokaye ko wasu gurbatattun da ake kira malamai karbar maganin mallakar miji to ku tabbata aurensu da mijin ba karko zaiyi ba, saboda maganin ba zaiyi wani tasiri ba ko da ya yi tasirin ma na dan lokaci ne yake lalacewa sai shi ma auren ya lalace, saboda an rike wanin Allah a matsayin zaiyi abinda Allah ne kaɗai zai iya yi ai kam dole aga sabanin abinda ake muradi.”

Direban yace: Ai wallahi suna zaman zamansu da mijinta lafiya bata rasa ci da sha ba komai yana mata amma da Maman Sultan tazo ta kalallameta da wasu kalamai sai matar ita kuwa ta yarda.

Labeeba: Ka ji irin matsalar ko… Wai ina hankalin wasu matan ke zuwa ne haka ! Ta yaya ina cikin zaman lafiya da miji na kawai kizo ki kawo min maganar zuwa wajan bokaye, yoo naje nace musu me ?

Direban: Ai kece kike da irin hankali da tunanin nan na Musulunci da hangen nesa, amma wasu tunaninsu kamar ba na mutane ba, yadda kikasan dabbobi, ai wasu ma gwara dabbobin da su a wasu lokutan.

Labeeba: Kaicoo. . ALLAH yakara tsare mana imaninmu. Amma to ita matar me take bukata ne da har za ta biyewa maganar Maman Sultan ta kaita wurin bokan?

Bani da lafiya

Direba: Ai Wai tunda tana zaman jin dadi da mijinta bari taje ta mallake shi sai abinda tace ayi za ayi, kuma ba ta son ya karo mata wata kishiya ta fi son zamanta ita kadai a gidan.

Labeeba tayi murmushi sai take cewa: Mu yanzu idan munyi wata magana akan rashin tsoron mu da kishiya sai ace ai don bamuyi auren bane shi yasa muke fadin haka, wai bamusan sharrin kishiya bane, amma ni banga abin tayar da hankali ba akan abinda Allah ya halastawa maza.

Direba: Allah Sarki…Ai ingaya miki bayan kwana biyu da amso maganin duk sai taga wata soyayya da nuna kulawa daga wajan mijin tana ja baya, abubuwan da ba ya yi mata su a baya na rashin mutumci da wulakanci yanzu kuma su yake yi mata, ingaya miki abubuwan duk suka dagule mata, lissafinta ya sauya gaba daya.

ABIN LURA

“Ai dama duk wanda ya sayi rariya ya san ba iya rike ruwa za tayi ba. Idan kabi wanin Allah ba makawa sai ka gamu da wayyo Allah, bin Allah shi kadai ne maganin wayyo ALLAH.”

(Insha ALLAHu a rubutu nagaba za muji ci gaban lamarin.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »