Lokutan Da Ya Kamata Kayi Shiru Da Bakinka

0 602

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

  • Kayi shiru lokacin da kake cikin fushi.

  • Kayi shiru lokacin da baka da ingantattun hujjoji na kare matsayinka.

  • Kayi shiru lokacin da baka da tabbas na ingancin labari.

  • Kayi shiru lokacin da kasan maganarka zata muzgunawa wani.

  • Kayi shiru a lokacin da ake bukatar ka saurara.

  • Kayi shiru lokacin da kake kokarin yin wasa da abinda ya shafi addini.

  • Kayi shiru lokacin da kasan zakaji kunyar kalmomin da ka furta nan gaba.

  • Kayi shiru lokacin da kasan kalomiminka zasu janyo maka zargi ko magana.

  • Kayi shiru lokacin da wasu suke tattaunawa kan abinda bai shafeka ba.

  • Kayi shiru lokacin da kasan abinda zaka fada ba gaskiya ba ne.

  • Kayi shiru lokacin da kasan maganarka zata zubar da mutuncin wani.

  • Kayi shiru lokacin da kasan maganarka zata haddasa kiyayya da lalata abota.

  • Kayi shiru lokacin da kake cikin mawuyacin hali.

  • Kayi shiru lokacin da kasan ba zaka iya magana ba sai ka daga murya.

  • Kayi shiru lokacin da kasan maganarka zata lalata tsakaninka da mahaliccinka.

  • Kayi shiru lokacin da kasan ba zaka iya kare maganar da ka fada ba a gaba.

  • Kayi shiru a duk lokacin da kasan abinda zaka fada Tsegumi ne ko yi da Wani ne ko Cin Zarafi ne ko Zagi ne ko kuma Bata Suna ne.

WANNE SHIRU KUKE IYA YI A CIKIN WADANNAN LOKUTA?

Gabatarwa: Abu-unaisa

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »