Bani Da Lafiya Kashi Na Arbain Da Shida (46) Matsalolin Da Kan Kawo Rashin Haihuwa

0 533

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Abu Arqam ya gyara zama yana cewa: muna suraronka Abu Ruwaihah.

Abu Ruwaihah: Sannan kuma irin sihirin nan yana haifar da abubuwa ga mace har mijinta yadda za su iya zama silar hana samun haihuwa (Amma duk sai da izinin ALLAH).

Ummu Arqam: Na’am Mallam, muna sauraren bayananka kuma muna fahimta sosai.

Abu Ruwaihah : Abubuwan nan su ne kamar haka:

1- A ranar da mace tayi tsarki daga al’adarta lokacin ne take releasing din kwayayen halitta “Ovulation” , amma sai ta rika jin kwatakwata ba ta son mijinta yakusance ta a lokacin, haka kurum sai ta rika jin haushinsa ba tare da wani kwakkwaran dalili ba a tsawon kwanaki 10 zuwa 14 bayan tsarkinta.

2- Ko ta rika ganin wani abu kamar jinin al’ada bayan kuma ta yi tsarki, ta yadda za su rika jefa mata wasuwasi akan tsarkinta ta rika ganin wani abu kamar na fita daga gabanta, har ta rika ji kamar jinin ya tsaya ko bai tsaya ba har lokacin “Ovulation” dinta ya wuce.

3- Ko su sanyawa mijinta wata irin kasala kamar ciwon kai da sauransu, tayadda za su hana shi kusantar matarsa ko ita ta ki amince masa a tsawon kwanaki 10 zuwa 14 bayan ta yi tsarki, lokacin da take yin “Ovulating”.

4- Mace tayi ta yawaita mafarkan haihuwa, jarirai, Aure, Daaji, rami Dawakai, taro, shanu da kuma ruwa.

5- Yawan samun sabani da yawan fushi tsakaninta da mijinta ba tare da wani dalili ba.

6- Ko ta rika yawan jin ciwuka kala-kala a kasan cikinta wajan mahaifa da bayanta, kuma ta rika jin kwaurinta yana nauyi ta kasa daga kafarta a wani lokacin, wannan kuma alamar kambun-baka ne da yake kama mahaifar mace.

8- Shedanu suna iya sanyawa mace matsalar “Hormonal imbalance”, ko su toshe mata “Fallopian tube” ta yadda za ayi ta magani amma aji shiru. ( Amma duk sai da izinin ALLAH.)

ABIN LURA

“Lallaikam Shedanu za su iya yin duk wani abu domin suga Sihirin da aka wakilta su akai ya yi aiki yadda yakamata, shi yasa akeson ma’aurata su dage da yin Azkaar da kiyaye dokokin ALLAH daidai gwargwado ba dare ba rana musamman ma Addu’a kafin saduwa da iyali kamar yadda Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya koyar da mu.”

(Insha ALLAHu za muji cigaban bayanin a rubutu nagaba.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »