Abu Labeeba yabashi amsa yana mai cewa: To, ni dai banace eh ko a’a ba gaskiya, amma yarinyar dai da kanta take kawo saurayi tace tana son shi, amma da zarar ance ya turo magabatansa ko magana sai ta yi nisa sai dai kaga kamar an kore shi ne, ba zai kara zuwa ba kuma, lamarin ya dagule ni abin har ya fara isata wallahi.
Abu Ruwaihah ya jinjina kansa yana cewa: Subhanallah…eh Lallaikam akwai matsala, amma yana da kyau ace na ga yarinyar don nakara ji daga gareta saboda akwai wasu tambayoyin da zata tabbatar min sai insan me da me yakamata nabata na shawarwarin da zata rike domin magance matsalar ta.
Abu Labeeba ya kamo hannun Abu Ruwaiha yana jinjinawa kuma yana godiya yake cewa:
” Yauwa Alhamdulillah, nima ai hakan naga zaifi tunda dai ni ba lallai ne ace na san komai game da matsalar ba, ita kuma Ummu Labeeba hankalinta ya fi karkata da ayi irin maganin da ya kaucewa hanyar Allah ni kuma na ki amincewa, shi yasa ma naga ta fara tsame hannunta akan lamarin yarinyar nan.”
Abu Ruwaihah: Ai fa… kaji matsalar wasu matan ko! Hmmm Wallahi matukar kana son gidanka ya tsaftatu daga kazantar shedanu kuma ALLAH ya shiga lamarin ku to karka kuskura ka amince akai yarinyar nan wurin da shari’ar Muslunci ta haramta zuwa da sunan neman magani.
Abu Labeeba cikin farin ciki da fara’arsa yace: Alhamdulillah ina matukar godiya Mallam, ina son arika bani kwarin gwiwa sosai akan lamarin nan.l, don gudun kar shedan yamin awon gaba da imani na.
Abu Ruwaihah yayi nurmushi yace: Ai hakki ne wannan dake kan Musulmi game da Dan uwansa Musulmi, yanzu dai ga wani abu nan da za ta rika yi kafin kuzo da ita wurina din….
Abu Ruwaiha yaci gaba da cewa: Ka samo bakin-Misk da Jan-Misk ko daya daga ciki, kamar guda 3 ko 5 (ka sanya kwalbar a cikin ruwan zafi har ya narke, sai ka zazzage shi ciki wata roba), sai a zuba Man zaitun a karanta musu Fatiha, Ayatul Kursiyyu, Ikhlas, falaqi da Nasi sau 3 ko 5 ko 7, idan za ta kwanta bacci sai ta rika shafawa a jikinta a guraben alwala kamar tana yin alwalar.
Abu Labeeba yayi godiya tare da farin ciki matuka, cikin fara’a yake cewa: Insha ALLAHu zamu fara aikata hakan kuwa a yau dinnan…
Abu Labeeba sukayi sallama da Abu Ruwaihah sai kowa ya wuce gida abinsa suka rabu cikin farin ciki da mutunta juna.
Abu Labeeba yana karasowa gida sai ya tarar da Labeeba ba ta gidan, ya tambayi Ummu Labeeba yana cewa:
“Ina Labeeba take ne kuma?”
Ummu Labeeba: Ai ko ka ga dawowarta daga makaranta kenan taci abinci sai tace za taje gidan kitso.
Abu Labeeba: Ayyoo ba matsala, Allah yadawo mana da ita lafiya. Ni bari inje Islamic chemist din can zan siyo Bakin Musk ne saboda na amai mata wani magani ne game da matsalar ta.
Fitar Abu Labeeba daga gida ke da wuya kenan sai ga Labeeba an kawo ta gida amma jiki a sanyaye ba lafiya, sai amai da gudawa abin dai ba dadi.
Nan take Ummu Labeeba ta shiga damuwa ta rasa yadda za tayi sai ta kira Abu Labeeba a waya ta sanar da shi abinda ke faruwa da Labeeba.
Abu Labeeba yayi maza-maza ya kamo hanya cikin wani irin yanayi na damuwa yana cewa: “Laa haula walaa quwwata illa billah…, Hasbunallahu wa ni’imal wakeelu.”
Yana karasowa gidan ne sai yatarar da Labeeba har ta yi bacci, sai yake tambayar Ummu Labeeba yana cewa:
” Wai me ke faruwa ne?”
Ummu Labeeba: To, ai kasan ta je gidan kitso ko? Jim kadan bayan fitar ka sai naga ankawo min ita ranga-ranga, tana ta yin amai, har wata take cewa; Wai Mayu ne suka kama ta, wata kuma tace: Ba mayu bane wannan Kambun baka ne.
To ni dai na kasa fahimtar kowanne daga ciki, saboda lamarin akwai ban mamaki, bamu kammala da matsalar nan ba sai kuma ga wata nan… Cikin kuka da hawaye Ummu Labeeba ke wannan maganar.
(Insha ALLAHu za muji abinda yafaru a cikin rubutu nagaba.)
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.
Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.
(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.)
Domin Ƙarin Bayani Game Da Darrusan Marubucin.
+2348031542026
https://t.me/Rismawymedicine
rismawy86@gmail.com