Bani Da Lafiya Kashi Na Sha Biyu (12).

0 591

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Labeeba ta gaishe su gaisuwa irin ta Addini cikin ladabi da girmamawa, su ma suka amsa mata cikin girma da mutumtawa.

Bayan ta wuce ne sai Abu Ruwaiha yake tambayar Abu Labeeba cewa:

“Wannan yarinyar  diyarka ce ko ne?”

Abu Labeeba: Kwarai kuwa diyata ce wallahi, ai itace wacce nake fada maka cewa tana fama da matsalar Jinnul Aashiq, kuma wallahi sun matsa mata sosai, yanzu kam Alhamdulillah ta fara samun sauki  tunda ma yanzu daga makaranta take.

Abu Ruwaiha: Wato Abu Labeeba ka san wani abu dangane da Jinnul Aashiq kuwa?

Abu Labeeba: A’a akramakallahu sai ka fadi, ina sauraronka.

Abu Ruwaiha: Wato sun kasu ne kala-kala, shi yasa za kaga wasu suna da wahalar barin jikin mutum har a rika tunanin kamar ba sa iya rabuwa da mutum ne.

Abu Labeeba: Eh Lallaikam na ga alamun haka. To amma me yasa ba sa iya rabuwa da mutum ne haka?

Abu Ruwaiha: Ai kasan wasu suna kama mutum ne ta hanyar Sihiri, sai kaga an turo su ne don su shiga jikin mutum su hana shi ko su hana ta Aure, ko su raba tsakanin mata da mijinta, ko su rikewa mace mahaifa ta kasa haihuwa, ko su lalatawa namiji ruwan maniyyinsa tayadda zai kasance ba zai iya haihuwa ba.

Abu Labeeba: Ya rike baki saboda mamaki, sai cewa yayi:  Na’ammm, sai yanzu nakara fahimtar matsalar, Subhanallah ! Wato lamarin nan dai ba karamin abu bane mallam?

Abu Ruwaiha: Kwarai kuwa, musmaman ma Idan mutum yazama ba ruwansa da Azkaar, ko bai cika yin ibada akai akai ba, to ka ga Waɗannan kam cikin sauki Sihiri ko shedanu ke shigar su, amma sai da Sanin Allah da yardarSA.

Abu Labeeba: Tabbas kuwa wannan haka yake, ALLAH ne mamallakin kowa da komai, babu abinda zai iya tabbata ko rashin tabbata sai da izininSA.

Abu Ruwaiha: Amma Abu Labeeba, ita yarinyar nan ta ka kamar menene yafi damunta ne a halin yanzu?

Abu Labeeba: To, a baya dai gaskiya abin ya yi yawa sosai kafin muje wurin wani mai magani, yanzu kam dai Alhamdulillah gaskiya ya yi sauki sosai, sai dai kawai rashin tsayayyen saurayi ne, saboda kaima dai ka ga yarinyar ta girma.

Abu Ruwaihah: Kwarai kuwa, ai burin duk wani nagartaccen uba yaga yarinyarsa tana gidan mijinta tun kafin tazama haka, su ma yaran da zaka binciki zuciyarsu za kaji cewa suna bukatar suyi auren. amma babu yadda za a iya da hukuncin Allah dole sai dai a zurawa sarautarSA  ido.

Abu Labeeba: Tabbas kuwa,  ai mu iyayen Labeeba mun fahimci haka kam, amma wasu iyayen ne ba sa fahimtar haka tayadda za kaga suna hantarar yaran tare da takura musu akan dolen dole sai sun fito da mijin aure, a haka wasu yaran da yawa sun iskance wasu kuma sun bar gidan sun bi duniya.

Abu Ruwaihah: Kaico… Ai ka ji matsalar mu, wato wasu iyayen fa suna taka muhimmiyar rawa wajan taimakawa lalacewar yaransu mata wani lokacin ma har da mazan.

Abu Labeeba:Tabbas kuwa Mallam, ai ni sheda ne, saboda akwai wata makobciyar mu yanzu haka yarinyar ta an rasa inda take sakamakon irin haka, wai shi ne kuma take so takai Labeeba wurin wani mai magani.

Abu Ruwaihah: Subhanallah..to kaga idan mutum na da hankali ai ba zai bi shawararta ba kam.

Amma kai yanzu Labeeba korar samarin nata take yi ne ko kuwa? Tambayar da Abu Ruwaihah yayiwa Abu Labeeba kenan.

Insha ALLAHU a rubutu nagaba za muji irin amsar da zai bashi

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »