Bani Da Lafiya Kashi Na Sha Hudu (14)

0 517

Abu Labeeba yaje yataba jikin Labeeba domin yaji yanayin jikin, yaji jikin dai sai ahankali shi ne nan take yakira Abu Ruwaihah a waya ya sanar da shi halin da Labeeba ke ciki, sai Abu Ruwaihah ya tambaye shi yana cewa:

“Ka samo wannan bakin misk da Jan misk din da nace a samo kuwa?”

Abu Labeeba: Kwarai kuwa suna a hannu na ma yanzu haka.

Abu Ruwaihah: To yanzu yadda za ayi idan kana da garin hulba a kusa da kai ka debi babban cokali 1 sai a zuba a ruwan zafi kofi daya,  sai a barshi ya jiku tukunna a ciki tswon mintuna 2 zuwa 3 har yadan huce kadan sai a karanta _FATIHA, AYATUL KURSIYYU, IKHLAS, FALAQI da NASI_ a ciki, iya adadin da za ka iya karantawa sai a zuba zuma daidai misali a bata ta fara sha, Insha ALLAHu za muga abinda zai faru da ita cikin mintuna kadan.

Ai kuwa Abu Labeeba ya aikata hakan, Labeeba tana shan maganin kenan sai ga shi jikinta ya jike da zufa, sai  amayar da maganin tayi.

Abu Labeeba ya sanar da Abu Ruwaihah cewar Labeeba fa amayar da maganin tayi.

Abu Ruwaihah yayi mamaki nan take yace: Subhanallah..! Amma bari dai in karaso gidan naga yadda lamarin yake.

“Wato; Matukar an baiwa mutum wannan hadin na garin HULBA cokali 1 a cikin ruwan zafi kofi 1 aka sanya zuma, aka barshi ya huce sai aka karanta FATIHA, AYATUL KURSIYYU, IKHLAS, FALAQI da NASI sau iya adadin da mutum zai iya, aka baiwa mara lafiyar yasha kamar rabin kofi, to na tabbata duk wani lungu da akayi ajiyar wani sihiri a cikin mutum sai wurin ya amsa DA YARDAR ALLAH.”

Abu Labeeba da Ummu Labeeba duk abin ya damesu matuka har Ummu Labeeba tana cewa:

“To ai kaine Abu Labeeba da kafiyar tsiya ga  cijewa akan abu, yanzu tun lokacin da nake ce maka a kaita wurin mai maganin da makobciyar mu Salaha ke bamu labarinsa ai da tuni yanzu yarinyar nan ta rabu da matsalar nan mu ma dai mu huta da wannan damuwar, amma kememe kahau kujerar na qi.”

Abu Labeeba yayi murmushi cikin tausasa murya yake cewa: Wato Ummu Labeeba ba lallaine a yanzu ki iya gane abinda nakeso ki gane ba game da matakin da na dauka na hana kai Labeeba irin wuraren maganin nan barkatai, saboda na gani da idanuwana ba sau daya ba kuma ba sau biyu ba abin ba dadin ji, yoo abinda ALLAH da ManzonSA suka haramta ai dama ba wani kyau ko albarka zaiyi ba sai dai ayi ta shan wahala anan duniya a lahira kuma asha azabar Allah, Allah yakara tsare mana imaninmu.

Suna cikin tattauanawar ne sai ga Sallamar Abu Ruwaihah nan ya ce: Assalamu alaikum wa rahmatullah !

Ummu Labeeba ta bude baki za ta amsa kenan sai Abu Labeeba ya rufe mata baki shi sai ya amsa da cewa: Wa alaikumus salam wa rahmatullah wa barakatuhu, dan jira kadan muna zuwa Ya Abu Ruwaihah.

Nan take Abu Labeeba yace da Ummu Labeeba: Ki gyara can da can sai ki shige cikin wancan dakin ki zauna.

Bayan sun kammala kimtsawar ne sai yayiwa Abu Ruwaihah izinin yashigo.

Abu Ruwaihah ya shigo yaga yatarar da Labeeba a zaune amma cikknnwani yanayin na sai ahankali, sai yace: A samo min ganyen magarya kwaya 7 zuwa 9

Aka tsinko sai ya ajiye su a gefe, yace : A samo ruwa cikin karamin botiki daidai gwargwado,

Shi ma aka samo sai yayi alwala yazo yayi karatun Alqur’ani (Wasu Ayoyi da surori) a cikin ruwan da yake cikin botikin, sai ya sanya ganyen magaryar nan a cikin ruwan ( bayan an dandake su kenan).

Bayan Abu Ruwaihah ya kammala ne sai yace: A debi kadan cikin kofi sai a bata ta sha ruwan, sai kuma ayi mata wanka da ragowar ruwan amma a wuri mai tsarki da tsafta.

Bayan an aikata hakan ne sai Labeeba taji jikinta ya yi sanyi, taji kasala ta kama ta tana tayin hamma sai ta koma bacci.

Abu Labeeba lamarin yabashi mamaki yana ta kallon Abu Ruwaihah yaji shin me zai ce ne kuma game da a lafiyar diyarsa.

(Insha ALLAHu a rubutu nagaba za muji abinda ya faru.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.)

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »