Huda : Ai ke dai kawai ayi sha’ani… Domin akwai wadanda za kiga suna kwashe duk matsalolin dake tsakaninsu da mazajensu wanda yake sirri ne daga shi sai ita waɗanda ko iyayensu ma bai kamata ace sunjisu ba, amma sai kiga suna kawowa kawayensu wai su basu shawara, kuma ba zasu iya nuna musu hanyar mafita ba sai dai wacce za ta kara kulle musu kai a cikin duhu a karshe kuma suyi batan bakatantan.
Labeeba: Allah ya kyauta, amma kam an shiga rububi domin gaskiya lamarin nan akwai cin-ruwa sai dai fatan ALLAH yakara tsare mana imaninmu.
Huda: Ai in karkare miki maganar yarinyar nan….Sai ma ranar da aka kawo mata kayan LEFE na gani na fada ingaya miki, sai naga tana ta daukar hotonsu tana kokarin watsawa a social media, sai na dakatar da ita nace mata : Wance kibi lmarin nan a hankali saboda mutum da ba kyau…
Ina ganin kamar na isa da ita saboda muna makobtaka kuma ni kawar yayarta ce…
Sai cemin tayi: Ya dai za ki hana ni na bayyanawa duniya farin cikin da nake ciki, ai ko Allah ma ya ce : Ka bayar da labarin Ni’imar da yayi maka.
Labeeba : Subhanallah.. Ina ga fa wallahi mutane suna fahimtar wannan Ayar a baibai, sai kiga suna fakewa da ita suna yin abubuwan da bai dace da Addinin ba… ALLAH yakara tsare mana imaninmu. Ameen.
Huda : Hmm kedai bari… Ai na yi kokarin fahimtar da ita amma naga ba za ta iya fahimta ba a halin yanzu, sai na kyale ta saboda har ta fara cemin ina yi mata bakin ciki ne da hassada don na ga an kawo mata irin wannan kayan.
Labeeba tayi murmushi tace : Allah Sarki…. rashin sani ne kawai wallahi.
Huda: An sanya ranar aurenta sati biyu masu zuwa, amma wallahi cikin satin nan komai ya rikice, auren da ba ayi ba kenan har yanzu kusan shekara 2 kenan.
Labeeba: Subhanallah…. Amma yar uwa ba kyau ganin irin wannan akwai matsalar Jinnul Aashiq a Lamarinta kuwa?
Huda tayi musmushi tace: Ai yar uwa ba komai ne ake dorawa Jinnul Aashiq ba musanman ma a irin wannan lamarin, saboda wasu abubuwan suna zuwa ne sakamakon sakacin da muke yi idan ALLAH yabamu wata dama sai kiga muna wasa da ita har tazo ta kufce mana.
Labeeba: Na’ammm, na fahimta kwarai da gaske yar uwa, gaskiya kam akwai wannan matsalar ma, saboda wasu matsalolin wallahy ba wai shan magani ne mafita ba, kawai mutum yayi nadama a lokacin da take da amfani kuma ya koma ga Allah da yawaita yin istigfari tare da ingantacciyar tuba daga abubuwan da yasan yanayi wadanda suke na sabon Allah ne.
Huda: Alhamdulillah, Lallaikam Labeeba kin fahimci batuna a daidai kenan kam, Allah yasa mudace.
Labeeba da mai Adaidaita ( Napep) suka hada baki suka ce: Ameen ya Rabb.
Huda : Mai Adaidaita don Allah idan ka karasa wajan layin can na biyu akwai, nan za ka sauke ni.
Labeeba: Allah Sarki, ashe ma nanne layin naku kenan?
Huda : Eh wallahy, bari dai nabaki lambar waya ta idan kin shirya kawo min ziyara kinga sai ki sanar da ni kafin kizo.
Bayan sun gama musayar lambobin su ne sai Huda ta sauka, sukayi sallama cikin mutunci da girmamawa.
Labeeba take cewa mai Adaidata sahun: Don Allah muyi sauri kar na makara ka ga yanzu saura mintina 10 Malami ya shiga ajin mu.
Mai Adaidata: Kar ki damu Hajiya Insha ALLAHu za mu kai kafin lokacin.
Bayan Labeeba ta shigo makarantar ne sai ta hango Bareerah zaune a karkashin wata bishiya, cikin fara’a nan take taje ta same ta.
Bayan sunyi sallama sun gaisa ne sai Labeeba take cewa: “Yar uwa me kikeyi ne anan haka naga kin zauna ke kaɗai?”
Bareerah: Wallahy na sha’afa ne banyi Azkaar din safiya bane shi yasa nakeyin su yanzu anan kafin Malami ya shiga ajin mu.
Labeeba: Allahu Akbar, nima kinga in ba yanzu da kika tuna min ba ai na sha’afa nima shaf !
Amma ni bari nafara yanzu kafin naje aji na kammala Insha ALLAHu, saboda malamin daf yake da ya shigo mana.
“Tabbas duk abinda kakeyi karka kuskura kakiyin Azkaar na safe da maraice domin neman Allah yabaka kariya daga sharrin halittunSA da kariyarSA kuma ya tsare ka daga sharrin su da tsarewarSA, ko da ka makara to a lokacin da ka tuna sai kayi shi, babban Azkaar shi ne Karatun Alqur’ani domin shi ne Azkaar din da yafi kowanne.”
(Insha ALLAHu za muji ci gaban bayanin a rubutu nagaba.)
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.
Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.
(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.)
Domin Ƙarin Bayani Game Da Darrusan Marubucin.
+2348031542026
https://t.me/Rismawymedicine
rismawy86@gmail.com