Bani Da Lafiya Kashi Na Sha Takwas (18)

0 523

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

“Musulunci Addini ne wayayye kuma masu bin tsarinsa har kullum su ne kaɗai wayayyu, boye sirri wata babbar dabara ce wacce Addinin Islama ya tarbiyyantar damu akai domin amfanin mu, wanda yayi watsi da wannan tsarin a karshe shi ne wanda lamarinsa ke dagulewa kuma ya tsunduma cikin nadamar da ba ta da amfani.”

Huda taga kwalla ta cika idanuwan Labeeba har tana yunkurin fitowa daga cikin idanuwan, sai ta zabura ta dafa kafadar Labeeba tana rarrashinta har take ce mata: Yar uwa, me ke damunki ne kuma haka? Me yasa za ki zubar da kwallarki mai daraja ne haka ?

Labeeba tayi murmushin dole take cewa: Ba komai yar uwa, wato shekaran jiya ne bayan na dawo daga makaranta sai naje gidan kitso, to a ranar an cika sosai a gidan kitson gaskiya, sai na kwance dankwali na ina tsefe kaina da gyara shi kafin layi yazo kaina, kawai sai ganin idanuwan kowa nayi a kaina kowa da abinda yake fadi.

Wata tace: Amma gashin nan naki gaskiya ya burgeni matuka.

Wata tace: Amma gashin ki ya fi nawa tsayi.

Wata tace: Ikon ALLAH, ni fa Shuwa-Arab ce amma ke bahaushiya ce na yi mamakin da naga kin fini tsayin gashi da kyau haka.

Wata ma har taba min gashin tayi tana cewa : Amma gaskiya Man da kike shafawa din nan ya karbe ki, ya sunan man nan ne….?

Huda ta tsaya kallon Labeeba tana ta mamaki, sai cewa tayi: To ke ya kikayi kenan a lokacin?

Labeeba tace: Ai kam na rasa ma abinda zance ne Saboda mamaki, ba’a fi mintuna 2 ba sai kawai ganina nayi a gida a kwance, amma duk bansan abinda yafaru ba kafin hakan, sai da na farka ne ma Umma ta ke bani bayanin yadda aka kawo ni gida rai a hannun Allah…Ya Subhanallah !

Huda tace: Haasha Lillahi ! Ai yar uwa kinyi kuskure kuma ba ke kadai bace ke aikata hakan, saboda mu mata sau da dama muna ganin ai ba wani abu bane don mun bayyana wani bangare na jikinmu ko wata ni’imarmu a bainar jama’a wadanda muka sani ko akasin su.

Balle ma yanzu da salon ya sauya sai dai kiga hatta ko BAIKO ( Engagement) ne akayiwa wata ko an kawo mata kayan LEFE, sai kiga ta dau hotunan su ko tayi stickers tana ɗorawa a status tana yadawa jama’a a social media ai gashi gashi…

Wata kuma tun auren saura watanni ko shekara take fara bayyanawa jama’a a social media kuma ita batasan cewa a cikin masu yi mata comments da like ba kowa ne masoyinta ba, a karshe sai dai kiga kawai lamarin ya dagule ya rushe a rasa dalili.

Labeeba : To ALLAH ya kyauta kuma yakara tsare mana imaninmu, wato kenan irin wannan abin akwia matsala….Ni ai sai nake ganin kamar ana sanyawa ne don a taya mutum murna ko?

Huda tayi murmushi sai tace: Wato kedai bari na baki labarin wata makobciyarmu game da wannan lamarin na san za ki tabbatar da abinda nake fada miki.

Labeeba kuwa ta kasa kunnenta tana sauraron abinda Huda za tace mata, sai Huda ta dafa kafadar Labeeba take cewa:

Wato yar uwa, ita wannan makobciyar tamu tana da saurayi wanda aurenta yake sonyi bilhaqqi, amma a cikin kawayenta kuwa babu mai saurayin da zai aura kuma dukkaninsu suna bukatar auren kamar me….

Kawai saboda rashin boye sirri na yarinyar nan sai kiga duk abinda saurayin ya bata na ihsani ko ya siyamata ko yayi mata wani alkawari irin na masoya sai kiga ta zo tana nunawa kawayenta tana labarta musu ai zai yi mata kaza da kaza.

Nan kuwa batasan yaqe kawai suke mata ba amma ta ciki na ciki, tana matsawa daga wurin za kiga suna ta sarar mata dunduniya, domin sun tsani tarayyarsu da saurayinta har zuciyarsu, rabuwar su kawai suke bukata.

Labeeba: Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.. Duniya ina za ki da mu haka kinga hassada ko! To su ina ruwansu da ita ne ma wai?

Huda tayi murmushi sai cewa tayin: Ai koma menene laifin nata ne, domin da bata fada musu ko nuna musu ba babu yadda za a yi susan me ke tsakaninsu da saurayinta balle har su kullaci wani abu a ransu.

Labeeba: Eh lallaikam fa dole ne sai bango ya tsage kadangare ke samun damar shiga. Allah ya kyauta.

Huda : Ameen ya Rabb. Ai ingaya miki ma rashin boye sirrin yarinyar ba iya nan yatsaya ba, sai da takai duk wata maganar da sukayi da shi a matsayin sirri daga shi sai ita na shirye-shiryen aurensu amma sai kiga tana zuwa ta kawowa kawayenta duk abinda sukayi da mijin da zata aura.

“Lallaikam duk wacce kukaga tana yin haka a ƙarshe za kuga auren ba ya yiwuwa bare yatabbata saboda ta budewa masu kambun-baka da mahassada kofar da za su iya yin duk abinda za su yi na shirke-shirken su sai su farraqa tsakaninta da saurayinta ko mijinta musamman ma idan suka kasance ba sa yin Azkaar sai kiga abin ya yi tasiri idan kuwa suna yin Azkaar a ko da yaushe to lallaikam sai kiga ALLAH ya basu kariya da Ingantacciyar kariyarSA.”

Labeeba: Kaico…Amma kam yan mata ana cikin tsaka mai wuya da rudani wallahi.

Huda : Hmmm au wai ke nan a tunaninki ‘yan mata ne kadai ke da wannan shirmen?

Ai ingaya miki akwai matan auren da sunfi yarinyar nan ma rashin rike sirrin gidan mazajensu, tayadda kuma hakan ke yin sanadiyyar wargajewar auren gaba daya saboda masu kambun baka da mahassada sun san abinda ake ciki..

Labeeba: Ton fah…! Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu.

(Insha ALLAHu a rubutu nagaba za muji abinda ake ciki.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »