Bani Da Lafiya Kashi Na Ashirin (20)

0 574

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

“Yanzu da yawa daga cikin mutane basu san menene Istihara irin wacce Addini ya koyar ba, sai dai kaga suna zuwa wajan wasu mutane ko wasu malamai wai ayi musu Istihara a duba musu idan abu kaza alkhairi ne a gare su ko akasin haka, sai kaga ana dulmiyar da su ana raba su da imaninsu kuma da yawansu rashin sani ne ke fara kaisu ga irin haka har suke a hallakar da su.”

Haka dai Maman Sultan tayi fice wajan tallatawa bokaye da malaman Tsubbu hajarsu a cikin makaranta wajan yan mata da matan aure har ma da wasu .daga cikin samarin, kaico…

Labeeba za ta shiga Aji kenan sai ta hangi su Maman Sultan ta tara wasu gungun mutane kai ka ce wani group discussion suke yi.

Labeeba dai mamaki yalullubeta saboda ta hangi wata yar ajinsu mai suna Ramlat a cikin gungun, amma bata dai kawo komai ba ta wuce aji abinta.

Har Malami na farko ya fito daga Ajin amma bataga shigowar Ramlat ba, mamaki ya ishi Labeeba ta koma gefe ta zauna tana ta karatun zuci tana cewa:

” Subhanallah ! Yanzu Ramlat din da na sani da kamewa da kuma gudun irin wannan shirme da shashancin da mutane ke yi na zuwa wajan irin Malaman nan amma itace tare da su Maman Sultan ! To wai ma me take ta karanta musu ne haka ? Amma dai kar na munana mata zato saboda babu kyau a rika munanawa mummuni zato, bari dai na ganta tukuna kafin na yanke hukuncin. “

Jimawa kadan sai ga Ramlat nan ta sami Labeeba a zaune sai tayi mata sallama Labeeba ta amsa mata sallamar.

Ramlat: Har malami ya fita ko Labeeba?

Labeeba: Kwarai kuwa ai bai ma jima da fita ba. Wai naga kamar ke nagani a can tare da Maman Sultan ko?

Ramlat: Kwarai kuwa ni ce wallahy ai sunan mu sa na samarin mu ne muka bayar, ita kuma zata kaiwa wani malami a unguwar su yayi mana istihara ko ALLAH zai sa a dace, saboda kinga yanzu samarin kwatakwata ba zama suke ba wallahi, kuma kar a garin zabe-zabe mutum yaje ya zabarwa kansa “MIJIN ALLAH BA NI”.

Mamaki ya ishi Labeeba sai cewa tayi: Laa haula walaa quwwata Illa bilLLAH !

Ramlat: Yar uwa, lafiya kuwa na ji ki kina hauqala ne kamar wata wacce bala’i yasama?

Labeeba: Ai dole nayi hauqala saboda wannan ma ai kamar bala’in yake, yanzu ace kamar ki wacce nake ganin kina da background na tarbiyyar Islama amma ki rasa inda za ki kai kukan ki ai aure sai wajan irin su Maman Sultan?

Ramlat : Labeeba don Allah kiyimin gamsasshen bayani don kinsa jiki na ya fara sanyi kwarai da gaske.

Labeeba: Ramlat kenan, Idan wata damuwa ta samu bawa abinda ake so ya tabbatarwa zuciyarsa shi ne: Ya tabbatar cewa lallaikam wannan daga ALLAH ne, Allah yana sane da abinda mutum ke ciki ba wai mantawa da shi yayi ba (matukar shi ma bawan ya baiwa ALLAH cancantarsa) kuma Allah ne kaɗai yake da ikon warware masa kuma ya yaye masa damuwar cikin lokacin da ya qaddara ba wai wanin ALLAH ba.

Ramlat: Tabbas na fahimci haka kuma na san da wannan Tauhidin sannan kuma ina godiya a tunatarwa.

Labeeba: To tun da kin fahimci tauhidin nan amma meye kuma na zuwa wajan maman Sultan har ki bayar da sunanki wai akai wurin wani malamai yayi muku istihara akan mijin Aure?

Ramlat tayi jigumm, ta kasa cewa komai sai cewa tayi: Hmmm Allah dai ya kyauta , wato rayuwar nan ce wallahy sai ahankali.

Labeeba taci gaba da bayani tana cewa: Ai wannan kwata kwata ba ma Istihara bace DUBA ne kawai wannan, kuma Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya tabbatar cewa: “Duk wanda yaje wurin BOKA ko DAN DUBA har ya gaskata abinda yace masa to ba shakka ya Kafircewa Abinda aka saukarwa da Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama, kuma wanda yaje bai gaskanta abinda yace masa ba, to sai ya yi kwana 40 yana ibada Allah ba ya amsa (har sai ya tuba).”

Ramlat: Subhanallah !Kenan kina nufin idan mutum yacewa wani yayi masa Istihara hakan ba daidai bane ba kamar yadda mu muka bayar da sunayen mu wajan Maman Sultan ?

Kafin Labeeba ta bayar da amsa sai ga Bareerah nan ta yi sallama,

Suka amsa mata sai suka bata wurin zama, bayan ta zauna ne sai dai ta fahimci kamar ba kalau ba, sai ta tambayi Labeeba tana cewa:

“Yar uwa lafiya kuwa naganku a haka kamar ba kalau ba?”

“Yanzu da yawa daga cikin mutane har ma da wasu cikin daliban ilimi musamman mata matsuwa da damuwa akan suyi aure ya sanya sun amincewa da irin wannan duban na shirme da shiriritar amatsayin istihara, ta yadda shedan ke yaudarar su da cewa za ayi musu istihara ne nan kuwa Duba ne irin wanda Muslunci ya haramta. Sai a kiyaye Allah yakara tsrare mana imaninmu.”

(Insha ALLAHu a rubutu nagaba za muji ci gaban bayanin)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »