Bani Da Lafiya Kashi Na Ashirin Da Uku (23)

0 542

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Sai lamarin Ramlah ya kara burge Labeeba saboda yadda take yin tambayoyin da za su yaye mata duhun da take ciki game da Istihara.

Sai Bareerah ta amsawa Ramlah tana mai cewa: Ai yar uwa ita Istiharar nan ba ta da wani kebantaccen lokacin da akace lallai sai lokacin ne za a iya yinta, amma wasu malamai sun nuna cewa ya kamata a yi ta a lokacin da ya tabbata a Nassi cewa ALLAH yana karɓar Addu’ar da akayi ta a lokacin, kamar kashi 1/3 na karshen dare, amma kuma za ki iya yinta a duk lokacin da kikaso matukar Shari’a ta bayar da damar yin nafila a lokacin. ALLAHU A’alam.

Ramlah ta jinjina kanta alamun dai tana gamsuwa da bayanan Bareerah ke mata.

Sai Bareerah taci gaba da cewa: Kuma ita Istiharar ba ta da wani adadin da aka iyakance cewa sau adadin ne za ayi ta, kawai yinta za kiyi ta yi ne har sai kinji tabbacin lamarin da kike yin Istiharar akai.

Murmushi gami da farin ciki ne kawai ke bayyana a kan fuskar Ramlah wanda yake nuna har zuciyarta ma hakan take.

Bareerah taci gaba da cewa: Kuma batun ta yadda mutum zai iya gane ko ya fahimci cewar ga sakamakon Istiharar sa yayi nan… Wannan ba kamar yadda da yawan mutane suka tafi akan cewa Mafarki ne kaɗai mutum zai yi akan lamarin sai a bayyana masa cewa gashi gashi nan … Wannan duk ba gaskiya bane kuma maganganun nan ba su da wani ingantaccen tushe.

Labeeba: To Bareerah yakamata kiyi mata bayanin yadda za ta fahimta sosai wata kila ma har ta iya samu itama ta fahimtar da wasu yadda lamarin yake.

Ramlah: Kwarai kuwa saboda ina da buƙatar hakan ne gaskiya, din nima mafarkin ne dai kadai naji ana cewa nanne mutum yake gane Sakamakon Istiharar sa.

Bareerah: Eh Lallaikam ya kamata akara haske, wato alama dai kamar yadda malamai suka yi bayani su ne: Mutum zaiji abin yana ta samun ci gaba ko yana kara shiga ransa ( To alama ce ta Alkhairin abin) ko kuma mutum yaji abin yana ta rushewa kuma yana kara fita a ransa ( To alama ce ta rashin Alkhairi ga abin.) ALLAHu A’alam.

Ramlah: Masha Allah, ALLAH yasaka muku da AlkhairinSa. Ameen ya Rabb.

Labeeba : Sai kuma wani karin bayani game da Istiharar, Ita ana yinta ne akan abinda ya shige ma mutum duhu game da sanin shin aikata hakan Alkhairi ne agareshi ko kuma akasin haka, amma idan alkhairin hakan ko akasin haka ya bayyana ga mutum to ba maganar yin wata Istihara anan sai dai amfani da abinda ya bayyana gare shi.

Ramlah: Fito min da abin a fili kuma kisanya min shi akan daidai don nakara fahimta mana yar uwa…

(Kwarai kuwa ba ma iya Ramlah ce kadai ke da bukatar kara fadada bayani game da wannan batun ba ….Insha ALLAHu a rubutu nagaba za muji yadda lamarin yake.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyarcewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu’aym)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »