ABIN LURA
“Matukar mutum ya nemi shawarar bayin ALLAH nagari kuma masana abinda zaiyi istiharar akai, sannan yayi Istiharar irin wacce Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya koyar kuma ya fawwalawa Allah lamarinsa, sannan yakarba kuma ya yarda da duk wani sakamakon da ya biyo bayan ISTIHARAR wanda ALLAH yatabbatar masa da shi, TO MAIYIN HAKA BA ZAI TABAYIN NADAMA A AL’AMURRANSA BA.”
Bareerah tayi murmushi sai tace: Wato Ramlah, abinda yar uwa Labeeba take ƙoƙarin fahimtar da mu anan shi ne: Misali kina da samari 2, amma dayan kowa ya tabbatar ba mutumin kirki bane, yayin da dayan kuma kowa ya tabbatar mutumin kirki ne, kema kuma duk kin tabbatar da hakan, to anan ba a bukatar yin wata Istihara tunda komai ya fito miki a fili a bayyane, yanzu dabara ta rage ta ki.
Ramlah: Na’am, Alhamdulillah….Lallaikam kinga anan idan mutum yabi son ransa saboda wani dalili na kashin kansa, to duk abinda yabiyo baya shi ne yajawa kansa.
Labeeba: Kwarai kuwa yar uwa, ashe dai kin fahimta.
Ramlah: Kwarai kuwa ai kam babu abinda zance muku sai mika godiya ta ga ALLAH da ya hadani da ku a matsayin mashawartan al’amurran rayuwa ta, ALLAH yasaka muku da alkhairinsa.
Suna cikin zaman ne sai ga Maman Sultan ta biyo ta gefen su sai ta hangi Ramlah, kai tsaye kawai tayi wurin na su ko sallama batayi musu ba sai cewa tayi:
” Ramlah, to ke muna ta jiranki akan ke kadai ce yarage ki bayar da abin sadaqar da za’a kaiwa Mallam sai kuma naganki anan.”
Ramlah tace: Ikon ALLAH, me ake bayarwa ne haka kuma Maman Sultan?
Mamman Sultan taga dai idan ta fadi a gaban su Labeeba za su iya hana ta yin wannan abin, sai cewa tayi: Ke dai bari mukara haduwa zan sanar da ke, saboda kinsan komai yana bukatar sirri.
Ramlah tace: Ayyah… Ai wadan nan da kike gani duk yan uwa na ne kuma ba su da wata matsala idan ma har kin fadi a gaban su, saboda ni da su ai duk hakan take ba wata matsala Insha ALLAHu.
Maman Sultan : Ah to bari dai na matso tunda kince haka, wato dama za a yanka wata dabba ne sai a cire zuciyar ayi amfani da ita, kuma kowacce mace ana bukatar ta yanko gashinta daga kowanne bangaren jikinta, da su ne za a fara yin maganin nan.
Labeeba suka hada ido da Bareerah suka sai Bareerah tace: A’uzu biLLAHI minasshaitaanir rajeem.
Itama Ramlah dai taga lamarin sai ahankali sai cewa tayi: To Maman Sultan za dai mu hadu zuwa anjima kafin mu tafi gida.
Maman Sultan ta tashi ta wuce abinta tace : To ba matsala sai mun hadun kenan.
Bayan wucewar Maman Sultan ne sai Bareerah tace: Ramlah kindai fara ji ko? Ai duk wani mai maganin da kikaji ya lissafo miki irin wadannan abubuwan to ba makawa BOKA NE, kaurace masa da duk wanda ya rabu da shi ita ce kadai mafita yadda za ki tsira da mutuncinki da kuma Imaninki.
“Sai ayi hattara, saboda da Imani ne kadai ake iya haduwa da Allah lami lafiya.”
Bayan kwana 2 ne sai ga Ummu Arqam ( kawar Ummu Labeeba tun kuruciya) ta zo gidan su Labeeba domin ta duba ta saboda ta ji labarin ba ta da lafiya,
Bayan sun gaisa ne sai Ummu Arqam take cewa: Ummu Labeeba kinga mu kam haihuwar har yanzu dai shiru wallahy, na yi magungunan har na gaji ina jin tsoron kuma kar naje na afka hannun mushrikai suje su hallakar da ni kuma su kaini su baro su raba ni da IMANI na, shi yasa kawai na dakata na fawwalawa Allah al’amarinsa.
Ummu Labeeba: ALLAH Sarki, gaskiya kam rashin haihuwa ba dadi, ace kowa yana ganin yaransa a gabansa amma kai sai ahankali. Amma matukar kina da rabon haihuwa to da yardar Allah za ki haihuwa lokaci ne kawai za kiyi hakurin zuwansa.
Akwai wani Mai magani mai suna Abu Ruwaihah shi abokin Abu Labeeba ne, zanyiwa Abu Labeeba magana Insha ALLAHu za a samu mafita.
(Insha ALLAHu a rubutu nagaba za muji shin a likitancin gargajiya wanda yake da alaqa da Muslunci akwai ciwon ko cutar da take kawo matsalar jinkirin haihuwa ko rashin haihuwa kuma ana warkewa ne daga hakan ko kuwa (Matukar ALLAH ya sanya mutum cikin wadanda suke haihuwa)? Insha ALLAHu za muji bayanin a rubutu nagaba.)
Domin Ƙarin Bayani Game Da Darrusan Marubucin.
+2348031542026
https://t.me/Rismawymedicine
rismawy86@gmail.com