Bani Da Lafiya Kashi Na Ashirin Da Biyu (22)

0 527

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Farin ciki ya lullube zuciyar Ramlat sai cewa tayi: wai kina nufin iya Addu’ar Istiharar kenan wannan kuma iya yadda akeyinta kenan ba karin wani abu daga baya?

Bareerah: Allah Sarki, ai iyakarta kenan yar uwa, ba wani yanka wata dabba, ba wata sadaqar masa ko dabino ko wani abu mai kama da hakan balle kuma ace a binne wani abu a wani wuri.

Labeeba: Masha ALLAH, wato Ramlat kindai ji gamsasshe kuma ingantaccen bayani akan yadda ake yin Istiharar nan a Muslunci ko?

Ramlat: Kwarai kuwa na ji yar uwa kuma na fahimta sosai, amma ni akwai wasu abubuwan da nakeson ayin min karin bayani akansu.

Bareerah: To Bismillah, muna sauraronki yar uwa.

Ramlat: Na ga an sanya wata baka (….) akace: ” mutum yafadi bukatarsa anan”, to kamar ya kenan?

Bareerah: Ai abinda ake nufi shi ne: Idan kina cikin karanta Addu’ar kikazo daidai wurin da akace ki fadi bukatar ki sai ki fadi bukatar ki ko da da hausa ne kuwa kamar haka:

  • “Wannan tafiyar da zanyi”
  • “Auren wance ko auren wane”
  • “Kasuwancin nan da zan fara”
  • “Siyan wannan abin da zanyi”

Da sauaran su.

Sai kuma kici gaba da Addu’ar har karshen ta.

Ramlat: Alhamdulillah, Allah yasaka muku da mafificin alkhairi. Amma yanzu kamar wasu haka don na san ba lallai ne su iya haddace Addu’ar nan ba, shi ne nace ko za su iya karantawa suna kallon takardar ko wayar da aka rubuta ko kuwa dole sai dai sun haddace ta din?

Bareerah: A’a, ba lallai ne sai wanda ya haddace Addu’ar bane kadai zai iya yinta ba, ko da baka haddace ba ma za ka iya karantawa a jikin littafi ko kuma wayar, amma dai anfi so mutum ya haddace ta din.

Ramlat: Masha Allah, ina godiya sosai. Amma shin da zarar an sallame sallah ne mutum kai tsaye zai fara addu’ar ko kuwa akwai wasu matakai da mutum zai bi tukunna?

Bareerah: Eh gaskiya kam, saboda ana so mutum ya mika godiya da yabo ga ALLAH ( kamar ya karanta suratul Fatiha da Ikhlasi da sauran yabo da kirarin da suka tabbata daga Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama) sai yayi Istigfari sannan yayi salatin Annabi Sallallahu alaihi Wasallama musamman na Ibrahimiyya, sai yafara yin Addu’ar kai tsaye.

Ramlah: Maasha Allah, amma sau nawa ne ake yin ita wanna sallar Istiharar kuma yaushe ne lokacin yinta sannan shin ta wace hanya ce mutum zai gane sakamakon Addu’ar?

(Insha ALLAHu a rubutu nagaba za muji yadda bayanin yake.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »