Bani Da Lafiya Kashi Na Ashirin Da Takwas (28)

0 518

ABIN LURA

“Wajibi ne ga dukkanin ma’aurata su san wannan tauhidin na samun haihuwa da rashin haihuwa duk ALLAH ne ke qaddara hakan, kawai ku dai duk wani abinda zai iya zama sababin da ALLAH zai sa ku samu haihuwar wanda ya dace da shari’arSA ( ba shirka ko tsallake umarnin Allah da ManzonSA ba) sai kuma ku dogara ga ALLAH kuma ku karbi duk abinda ya tabbatar muku da shi ko da ya sabawa abinda zuciyar ku ke muradi.”

Ummu Labeeba: Hmmm Allah Sarki godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin da ya gagari kowa da komai kuma yake tabbatar da abinda yaga dama a lokacin da yaga dama ba tare da taimako ko shawarar kowa ba.

Ai wato Ummu Arqam nima ai ba jayaya nayi masa ba, ce masa nayi: Lallaikam maganar Allah babu ja a cikinta, ai abu Labeeba duk wani Musulmin kwarai ya san da hakan amma dai ya kamata mu gwada neman maganin mugani tunda dai ba haramun bane neman maganin, kuma a zahiri likitoci sun tabbatar mana cewa bamu da wata matsala ni kuma ga abinda nakeji nan na ciwon da yake damuna ina jin wata kila su ne silar wannan jinkirin haihuwar tamu. ?

Sai cewa yayi: Wato ba wai na ki maganar ki bane Ummu Labeeba, ina so ne dai ki fahimci wannan tauhidin kuma ki sanyawa zuciyarki cewar ko da munyi maganin sai dai yazama sila domin duk fadin duniyar nan babu wani magani ko mai maganin da ya isa yabayar da haihuwa sai ALLAH shi kadai idan yaso, sai dai kawai mu dauki maganin a matsayin sila ko sanadin samun haihuwar mu.

Nace masa kwarai kuwa Abu Labeeba na amince da hakan. Sai cemin yayi: Insha ALLAHu zuwa gobe zanje wurinsa domin yace min zaiyi tafiya ne zuwa sati mai zuwa, tunda shi ne nake kyautata masa zaton za a samu maganin da bai sabawa Shari’ar ALLAH ba, da ma gujegujen da nake yi kenan kar muje a garin son haihuwa ta kaimu ga shirke-shirke a karshe mu rasa Rahamar ALLAH da Imaninmu .

Ai kuwa yana zuwa sai naji ya kirani a waya yana cewa: Abu Ruwaihah yace ayimiki tambayoyin nan kamar haka:

1- Kina fama da ciwon kasan cibiya da ciwon mara da ciwon baya daga kasa setin mahaifa?

2- Kina fama ne da mafarkin namijin dare ko na haihuwa, ko na shayarwa ?

3- Jinin al’adarki yana miki wasa ne ko kina yawan zubar jini ?

4- kina jin zazzabi ne sai kuma kiji jikinki ya yi zafi sosai?

5- Kina jin ciwon kai ne na bari daya ko na duka kai din?

(Insha ALLAHu a rubuta na gaba za muji irin amsar da Ummu Labeeba ta basu)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »