Bani Da Lafiya Kashi Na Ashirin Da Daya (21)

0 23

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

“Ya zama lallai kowa ya tabbata ya koyi kuma ya koyar da iyalansa Sallah da Addu’ar istikhara yadda Annabi yakoyar da Sahabbai ita, domin gujema shirme da shiriritar bokoye da yan duba da wasu ke dauka a matsayin itace Istikhara. Allah yasa mudace.”

Labeeba tayiwa Bareerah bayanin da suke tattaunawa ita da Ramlat sai Bareerah tace: Subhanallah! Ke kuwa Ramlat a garin yaya hakan ta faru…. me yakai ki wajan wannan matar ne?

Labeeba: Wallahy kuwa kema dai kin fada… Yanzu nima mamakin da nakeyi kenan akan me zai hana ita tayi Istiharar da kanta a maimakon ta baiwa wani yayi mata wanda shi kuma ba ma yadda Addini ya koyar zaiyi ba, wani fa har aljanu ake hadawa da su.

Bareerah: ALLAH Sarki…Ai ke kuwa Labeeba ba kowa ne ya iya Addu’ar nan ba, wani ya san anayi amma baisan yadda ake yi ba kuma ba abin mamaki bane don kinga wani ya ce bai iya ba, saboda haka shi ya taso ya fahimci ai da zarar ance Istihara to kawai a duba aga alkhairi ne ko kuwa..

Ramlat dai tayi shiru tana ta sauraron su, abin yabata mamaki sosai sai cewa tayi: To yan uwa ni duk kun sanyani cikin duhu , ku gane mini hanya mana na fita daga cikin wannan yanar da gizogizon Maman Sultan yayi min a zuciya.

Bareerah ta dafa kafadar Ramlat tace: Yar uwa ki kwantar da hankalinki ai hakkin duk wani musulmi ne ya sanar da Dan uwansa Musulmi abinda baisani ba, duk dai saboda a gudu tare kuma a tsira tare.

Ramlat: Alhamdulillah.. ai ni ina ganin lamarin Istiharar nanne kamar wani babban abu ne dabam wanda ba kowa ne zai iya ba sai mutane na musamman ko wasu kebantattun malamai.

Barrerah da Labeeba sukayi murmushi sai Bareerah tace: Allah sarki..ai kowa ma na musamman ne kowa zai iya da kansa, kawai abinda za kiyi shi ne: Kiyi alwala cikakkiyar alwala, sai kiyi Sallah nafila raka’a 2 ( a lokutan da ake yin nafila), bayan kin sallame sallar sai ki daga hannu kiyi wannan Addu’ar kamar haka:

DA LARABCI

اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْتَخِيرُكَ بِعِلْمِكَ، وَأسْتَقْدِرُكَ بِقُدْرَتِكَ، وَأَسْألُكَ مِنْ فَضْلِكَ الْعَظِيم، فَإِنَّكَ تَقْدِرُ وَلا أَقْدِر، وَتَعْلَمُ وَلا أَعْلَم، وَأَنْتَ عَلاّمُ الغُيوبِ، اللّهُمَّ إِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا اْلأَمْرَ- (———- )- خَيْرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، عَاجِلِهِ وَأَجِلِهِ فَاقْدُرْهُ لِي وَيَسِّرْهُ لِي ثُمَّ بَارِكْ لِي فِيهِ، وَإِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا اْلأَمْرَ شَرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، فَاصْرِفْهُ وَاصْرِفْنِي عَنْهُ وَاقْدُرْ لِي الْخَيْرَ حَيْثُ كَانَ ثُمَّ أَرْضِنِي بِهِ.”

DA HAUSA

“Allahumma innee astakheeruka bi’ilmika, wa-astaqdiruka biqudratika, wa-as-aluka min fadlikal-‘azeem, fa-innaka taqdiru wala aqdiru, wata’lamu wala a’lamu, wa-anta ‘allamul ghuyoob, Allahumma in kunta ta’lamu anna hazal-amr -(sai ku fadi bukatar ka anan )- khayrun lee, fee deenee wama’ashee wa’aqibati amree faqdurhu lee, wayassirhu lee, thumma barik lee feehi, wa-in kunta ta’lamu anna hazal-amr sharrun lee fee deenee wama’ashee wa’aqibati amree fasrifhu ‘annee wasrifnee ‘anhu, waqdur liyal-khayra haythu kaana, thumma ardinee bihi.”

(Insha ALLAHu za muji karin bayani a rubutu nagaba)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »