Bani Da Lafiya Kashi Na Ashirin Da Shida (26)

0 588

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

ABIN LURA

“Ya kamata mai fama da matsalar jinnul Aashiq ta rika yin magani da Azkaar tun kafin tayi aure, domin idan tayi biris da lamarin har tayi aure kuma ta samu juna-2 to da alamar jaririn zai iya kamuwa da lalurar Jinnul Aashiq din sai yazama na gado, matukar ba sa yin Addu’a a lokacin saduwar aure ita da maigidan kamar yadda Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya koyar, ko kuma da zarar an haifi yaron a rokar masa neman ALLAH yatsare shi daga sharrin shedanu.”

ALLAHu A’alam

Ummu Arqam tayi shiru ta kasa kunnuwanta tana sauraron abinda Ummu Labeeba za tace mata, sai cewa tayi: Ina jinki yar uwa.

Ummu Labeeba: Wato nima a baya can tunnina budurwa kafin na auri Abu Labeeba na yi fama da matsalolin nan na jinnul Aashiq amma kasantuwar ni kwatakwata ban kawo wata matsala bace saboda ni ba sa wani tashi balle nace ina da su, alokacin ma bansan alamomin jinnul Aashiq din ba sai bayan da na haifi Labeeba itama ta rika fama da irin matsalar.

Ummu Arqam: Allah Sarki, wato haka fa wasu ke fama da irin haka saboda su basu ma san matsalar bace har sai abin ya ci tura kuma azo lamari na neman ya gagari kundila.

Ummu Labeeba: To a lokacin kafin nayi aure gaskiya ba ruwa na da wani Azkaar, sallar ma ni ba wani damuna tayi ba balle na rika amfani da su Man zaitun ko misk da sauransu, kawai ahaka nayita tafiya da rayuwata a hargitse ba tsari, saboda ni a tunani na ai banyi aure ba tukuna balle Addini ya dameni har na rika yin Sallah yadda yakamata.

Ummu Arqam: HasbunaLLAHU wa ni’imal wakeelu. Wato lamarin nan haka fa har yanzu wasu yan matan suna fama da rashin yin ibada musamman ma Sallah suna wasa da Sallah matuka wallahy, kuma hakan yana matukar yiwa rayuwarsu illa.

Ummu Labeeba: To fa kinga inda matsalar ke somowa nan, tayaya kuwa mutum ba ya Sallah yace kuma Allah zai bashi kariya daga shedanu, ai a lokacin ne ma shedanun za su kara alaqantuwa da mutum su zama amininsa.

Ummu Arqam: Allah Sarki, Allah yakara tsare mana Imaninmu kuma ya tsare mu da tsarerwarsa, Ameen ya Rabb. Amma Ummu Labeeba ke tayaya kenan kika rabu da wannan matsalar ne?

(Insha ALLAHu zanyi muku bayanin cigaban lamarin a rubutu nagaba)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »