Bani Da Lafiya Kashi Na Ashirin Da Bakwai (27)

0 531

Ummu Labeeba: ALLAH Sarki, ai wato bayan aurena sai da nayi shekara 3 ko batan wata bantaba yi ba a gidan Abu Labeeba, abin dai ya dameni sosai saboda na ga kawayena kowacce ta haihu sai ni kadai har mutane suka fara wasu kananan maganganu akan lamarin.

Ummu Arqam: Ai kam haka dai wasu mutanen suke wadanda ma ba ruwansu cikin lamarin sai kiga suyita tsoma bakinsu a ciki, ba ruwansu da fadin Alkhairi sai dai akasin haka, Allah yakara tsare mana imanin mu.

Ummu Labeeba: Abu Labeeba dai shima hankalinsa ya kasa kwanciya saboda mun kasa gane waye ke da matsalar ne a tsakanin ni da shi.

Ummu Arqam: Ince dai kunje asibiti anyi gwajegwaje an duba lafiyar ku akan haka ko?

Ummu Labeeba: Kwarai kuwa, wallahy munjajje asibitoci da dama na gwamnati da masu zaman kansu kuma an duba kowane daga cikinmu lafiya kalau yake, har likitocin ke cewa kowannen mu zai iya haihuwa ba mu da wata matsala.

Ummu Arqam: Ikon Allah kenan.

Ummu Labeeba: Amma kuma ni gaskiya na san ba lafiya ba, domin yadda nake yin ciwon mara mai tsanani da kuma ciwon baya mai tsanani duk a lokaci guda yadda kikasan wata mai naquda kuma al’ada ta sa tayita rikicewa har na rasa gane lissafin ma wallahi, sai nakasa jurewa cewa Abu Labeeba nayi: “Ko za ka sanar da abokinka ne mai maganin gargajiya na Islamic sai mu gwada shi mugani ko kuwa.”

Ina fada masa haka sai cemin yayi: Ummu Labeeba kenan, ina so kisani cewa akwai ma’auratan da sukayi aure sama da shekaru 10 wasu kuma 20 ko sama da haka amma ba haihuwar sai daga baya ALLAH ya nufe su da haihuwar.

Ki kwantar da hankalinki Ummu Labeeba, wato ita haihuwa lokaci ne wanda ALLAH ya qaddara matukar lokacin baiyi ba babu yadda za ayi a haihu, amma da zarar lokacin ya yi sai kiga an haihuwa komai daren dadewa kuwa. ALLAH ne ke bayar da haihuwa ga wanda yaga dama kuma ya hana wanda yaga dama da hikimarSA, kamar yadda yake cewa:

ALLAH YANA CEWA

“Yana bayar da kyautar haihuwar diya mace ga wanda yaso, kuma ya baiwa wani d’a namiji ko kuma ya gauraya musu maza da mata kuma sai kaga ya bar wani ba ya haihuwa.”

Ummu Arqam dai lamarin ya burgeta sosai sai cewa tayi: Wato Ummu Labeeba ki godewa ALLAH da ya azurta ki da miji mai fahimtar tauhidi haka, yoo ni ko haka ma nasamu ai sai hankalina yarika kwanciya domin ba abinda zai rika dagamin hankali saboda ana yiwa zuciyata yayyafin tauhidi ai dole takara samun nutsuwa.

(Insha ALLAHu za muji ci gaban bayanin a rubutu nagaba.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »