Bani Da Lafiya Kashi Na Ashirin Da Biyar (5)

0 596

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Ummu Arqam tayi murna tare da farin ciki matuka da jin wannan batun daga wajan Ummu Labeeba, sai take cewa : “Wato Ummu Labeeba wallahy abin nan idan nace miki ba ya damu na na yiwa kaina karya, saboda ni abinda yafi damuna ma game da lamarin shi ne: Yadda dangin mijina ke nunamin tsana, habaici ga muzgunawa duk wai saboda me yasa ban haihu ba har yanzu ! Ni kuma ba nice zan baiwa kaina haihuwar ba.

Ummu Labeeba: Subhanallah ! Wai yaushe mutane za su daina wannan jahilcin ne haka? Ai hakan yana nuna basu yarda da ALLAH ne ke yi komai ba kenan.

Ummu Arqam: Hmm ke dai kawai ayi sha’ani, wallahi a cikinsu ma akwai wadanda suke da ilimin Addini na yi zaton samun sauki daga gare su saboda ina tunanin su sun fahimci wannan tauhidin, duk sai naga sabanin yadda nake tunani ne su ma sun biyewa wawayensu.

Ummu Labeeba: Kaico…. Amma dai ALLAH wadaran naka ya daidaice ! Mutane sai kiga yanzu kawai karatun ya zama kamar wata kwalliya ce ba abinda ake yin aiki da shi bane sai dai ayi ado da shi.

Ummu Arqam: Wallahy kuwa, domin wata rana ma sai naji zaman auren ma ya ishe ni saboda irin maganganun da suke ta aike min da su, gwara nayi zama na ni kadai na san ba ni da wata matsala ko damuwa balle zuciyata ta kasa zama kalau.

Ummu Labeeba tayi murmushi sai cewa tayi: A’a yar uwa kar kiyi haka kuma kidaina irin wannan tunanin haka ya kamata kibaiwa shedan da shedanu kunya, kawai kisa a ranki cewa ALLAH ne ke bayarwa kuma kema bai manta da ke ba, kuma zai baki rabonki matukar ya tsaga da ke, kawai hakuri za kiyi da daukar sabubba wadanda suka inganta a addinin ALLAH kuma a dogara ga ALLAH mai kowa mai komai.

Ummu Arqam: Insha ALLAHu kuwa, na gode da wannan shawarar taki yar uwa, Allah yasaka da alkhairi.

Ummu Labeeba: Aameen ya Rabb. Wato Ummu Arqam nima da kika ganni nan na sha fama da wannan matsalar ta rashin haihuwa, har na fitar da rai amma sai daga baya ALLAH yabani Labeeba. Tabbas yana da kyau na fada miki yadda lamarina yake don kema ki kara nutsuwa akan taki matsalar kuma ki yarda da Allah ne ke yin komai ba bayin Allah ba.

ABIN LURA

“Matukar mutum ya yarda da ALLAH ne kadai ke da ikon tabbatar da komai ba bayin Allah ba, kuma yayi hakuri akan jarrabawar da yake fuskanta sai ya mika Al’amrinsa ga ALLAH sannan yayi riko da sabubban da suka inganta a musulunce, sai kaga ALLAH ya bashi mafita wacce zaiyi farin ciki da ita ta inda bai taba tsammani ba”.

(Insha ALLAHu a rubutu nagaba za muji abinda Ummu Labeeba ta fadawa Ummu Arqam)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »