Kullum Labeeba idan taje makaranta sai ta rika yin bacci ga kasala da take ji a jikinta da hamma, musamman ma idan malami ya shigo cikin class an fara karatu, lamarin da yasanya wani malaminsu (mai suna mallam Zaidu) ya lura da yanayinta, tun yana yi mata fada har ya gaji sai ya lura kamar dai ba kalau ba.
Hakan tasanya sai da Malam Zaidu yayi tattaki yaje har gidan su Labeeba domin ya gana da mahaifinta Abu Labeeba dangane da batun diyarsu Labeeba.
Bayan sun kammala gaisawa ne sai suka ci gaba da tattaunawa kamar haka:
Mallam Zaidu: Abu Labeeba wai anya kuwa Labeeba lafiya take?
Abu Labeeba: Toh ! Ni dai lafiya nabarta mun rabu lafiya lokacin da za ta tafi makaranta, amma bansan abinda yafaru ba, saboda ka san ance “Baya ba ta da kadan.” Shin wani abu ne yafaru da ita ne Mallam?
Mallam Zaidu dai baiyi wata wata ba nan take yafara bayani kamar haka:
Eh…toh.. Alhamdulillah ! Gani ne nake yi daga bayannan kullum Labeeba idan tazo makaranta ba abinda take yi sai bacci kuma tayi ta complain akan wai ta gaji ita gida take son zuwa, ga yawan bacin rai da fushi wanda abaya ba haka take ba, na yi fadan har na gaji shi ne nace bari dai nazo na same ku ko akwai wani abinda ke faruwa ne da ita.
Abu Labeeba yayi tagumi saboda dai shi ma abin ya bashi mamaki sai can yace: To Malam ! Wallahy nima dai ban gama fahimtar lamarin Labeeba ba gaskiya saboda mu ma kanmu abinda muke ta complain akanta kenan, saboda mu tun a baya muna kallon abin kamar ba komai ba, amma yanzu mu ma lamarin ya fi karfin mu a haka dai muka barta.
Amma yanzun nan zan tuntubi Ummu Labeeba naji ainihin dalilin, saboda ka san su mata ne kullum suna tare da su, (cikin dariya) mu kuma muna can waje muna nema.
Mallam Zaidu ya rike baki cikin mamaki yace: Au ! Wai kana nufin baku taba zama kai da Ummu Labeeba kun tattauna matsalar Labeeba ba tun farkon da kuka fara ganin sauyi a rayuwarta?
Abu Labeeba: Hmmm Mallam kenan, yoo ai mu a baya bamusan da cewa damuwa ce haka ba, amma tunda dai yanzu mun farka bari na shiga cikin gida, Insha ALLAHu zan waiwayoka akan batun zuwa anjima.
“Lallaikam wasu iyayen suna yin babban kuskure wajan rashin lura da sabon yanayin da yaransu ke nunawa game da lafiyarsu tun suna kanana, sai sun girma kuma abin yazo yana nema ya gagari kwandila.”_
Abu Labeeba ya shigo cikin gida jikinsa duk ya yi sanyi sosai, sai yake cewa Ummu Labeeba:
Wai yarinyar nan me ke damunta ne haka? Saboda yanzu malaminsu yazo min da bayanin cewa ko a class ma aikinta kenan?
Ummu Labeeba: To Abu Labeeba abin dai ga shi nan, saboda yanzu haka ma baccin take yi tun dawowarta daga makaranta tace min zazzaɓi take ji, kullum dai aikin kenan.
Abu Labeeba,: Wai anya kuwa matsalar nan tata kalau kuwa? Wai kuma ke baki taba hankaltar wani abu a tattare da ita ba a matsayin ki na uwa kuma mahaifiyar ta?
Ummu Labeeba: Toh ! Bana ce a’a ba gaskiya, domin tun da ina da cikin Labeeba na fuskanci abubuwa da dama na ban mamaki da firgici, saboda gaskiya hatta Ibada ma sai da tazo tana gagara ta yi, ga shi ba ruwa na da Addu’ar neman taimakon ALLAH akan ya tsere min wannan cikin nawa daga sharrin halittunSA kuma ya saukar da ni lafiya.
“Lallaikam wasu masu cikin suna fama da wannan matsalar ta rashin yin Addu’ar ALLAH ya tsare musu abinda ke cikinsu kuma ya saukar da su lafiya, duk daga cikin Hikimar da ALLAH yabar mai ciki tayi Sallah da sauran ibadu cikinsu akwai damar yin Addu’a da bautar ALLAH tukuru saboda tana cikin masu tsananin bukata, Kuma tana dauke da abinda babu mai iya tsare sa kuma yasan halin da yake ciki sai ALLAH Ubangijinsa.”
(A rubutu na gaba zamuji irin abubuwan da Ummu Labeeba take ji a lokacin da take dauke da cikin Labeeba.)
Allah yasa mudace kuma yakara tsare mana imaninmu.
Domin Ƙarin Bayani Game Da Darrusan Marubucin.
+2348031542026
https://t.me/Rismawymedicine
rismawy86@gmail.com