Ba Ni Da Lafiya Kashi Na Uku (3)

0 571

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Sau da dama wasu cututtukan suna samun yara ne tun a lokacin da. Ake dauke da cikinsu, shi yasa ake son uwa mai dauke da ciki ta dukufa ka-in da na-in wajan jajricewa da neman magani da zuwa ganin likita da kuma uwa uba neman taimakon Allah akan halin da ya ɗora mata kuma ya basu kariya ita da shi daga sharrin halittunSA kuma YA saukaka mata hanyar sauke shi cikin lafiya da kwanciyar hankali ba tare da wata matsala ko nakasa ba.

Ummu Labeeba taci gaba da cewa: Wato Abu Labeeba a lokacin gaskiya na fuskanci wasu mafarke-mafarke masu ban tsoro, kuma ga shi kullum da yamma ko cikin dare sai na fita na bi ta gefen maqabartar nan ta unguwar mu na je debo ruwa a fanfo, idan nadawo kuma sai kaga na yi mafarkin maqabartar da ruwa har ma da na shanu.

Abu Labeeba cikin bacin rai yace: To ke kuma Ummu Labeeba tun ba yau ba fa na hanaki fita cikin dare amma ba kyajin magana wallahy, hatta dibar ruwan nan ma da daddare na hana ki shi yasa ma na sanya yan ga-ruwa su rika kawo mana ruwan nan ina biyansu saboda matsalar cikin da kike dauke da shi, amma duk da hakan ke sai kin fita kin debo ruwan nan.

Ummu Labeeba: Ikon Allah kenan, wai dama mai ciki ba a son tana fita cikin dare ne?

Abu Labeeba: kwarai kuwa, musamman ma ta rika bi ta maqabarta da wurin ruwa.

Ummu Labeeba: Yoo ko hakan yana da illa ne dangane da abinda take dauke da shi don gaskiya Ni ban ma sani ba? Ta yiwu ga daga nan matsalar take….

“Lallaikam masu ciki ya kamata su rika kiyaye duk wani abinda masana suka ce zai iya cutar da lafiyar su da ma lafiyar abinda suke dauke da shi a cikinsu, kuma su rika daukar shawarwarin su matukar basu sabawa Shari’ar Allah ba.”

Abu Labeeb yayi murmushi yace: Yoo ai Ummu Labeebah nima kaina abubuwan nan da kikeji ina fadi ba wai  sanin harkar maganin nan nayi ba, na dai taba jin wani malami ne yana bayanin irin haka shi yasa nima na rike su, amma dai ya kamata muje wajan Masana wannan harkar domin su kara wayar mana da kai ko ma samu maslaha akan matsalar yarinyar nan, saboda Addini ya koyar da mu cewa:

“Mu rika tambayar ma’abota sanin al’amari idan har mu bamu sani ba.”

Ummu Labeebah: Tabbas kuwa wannan haka yake, ka ga shi ne mafi zaman lafiya da kuma kaucewa afkawa cikin hallaka.

 To yaushe ne za muje kuma ina za mu fara zuwa ne? Tambayar da Ummu Labeebah tayiwa Abu Labeebah kenan.

Bude bakin Abu Labeebah kenan zaiyi magana sai suka ji wani sauti mai tsananin qara daga cikin dakin da Labeeba ke kwance ana cewa: SUBHANALLAH !!!

Yunkurar da za suyi kenan domin sune suga lafiya kuwa.. Sai ganin Labeebah sukayi ta fito a guje ta zo ta rirriqe Ummu Labeebah cikin tsoro tana cewa : Ga tanan ! Ga tanan !!!

Abu Labeeba cikin furgici amma ba abinda ke fitowa daga bakinsa sai: A’uzu biLLAHI minasshaitanir rajeem, HasbunALLAH wa ni’mal wakeelu…

“Haka akeso mu rika ambatar sunan Allah da girmama SHI tare da tabbatar masa da cancantarSA a duk lokacin da wata musiba ko wani al’amari na firgici da tsoro ya riske mu.”

A gefe daya kuma Ummu Labeeba tana ta kabbarori da Addu’a, ba jimawa ne sai ga Labeeba ta farfaɗo hankalinta ya dawo jikinta.

Tana duba jikinta tana tambayar cewa: Ummu lafiya kuwa? Me ya faru ne haka?

Sai Ummu Labeeba tace: Ba komai Labeeba,

Abu Labeeba yace: Wato Labeeba mafarki kikeyi ne haka a cikin baccin naki ko kuwa?

Labeeba tayi ajiyar zuciya tace: Hmmm ! Toh Abba, ni kaina gaskiya na rasa me ke damuna, saboda tun ba yau ba nake ta jin jikina dai ga shi nan ga irin shi, kuma ga mugayen  mafarkan da nake fuskanta.

Ummu Labeeba tace: Abu Labeeba na ji wani malami a can layin yana fassarar mafarkai, ko dai za mu je ne sai a fassara mana  ma’anar mafarkin da Labeeba take yi ko za mu iya shawo kan lamarin da wuri ko kuwa?

Abu Labeeba yayi murmushi sai cewa yayi: Yoo ai irin fassare fassaren mafarkan nan sau da dama ba inda suke afka mutane sai cikin rashin kwanciyar hankali da nutsuwa a koda yaushe, a karshe kuma su hallakar da wasu.

Ummu Labeeba: To me yakamata muyi ne tunda dai ka dakile wannan hanyar?

“Tabbas an hallakar da wasu mutane da dama wajan zuwa ana  fassara musu duk mafarkan da sukeyi, saboda haka yakamata mutane su rika kauracewa zuwa wajan wasu suna fassara musu duk mafarkan da sukeyi saboda akwai gurbatattu wadanda suke kai mutane ga mahallaka kuma su baro su acan, abinda yafi dacewa kawai shi ne mubi abinda Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya koyar da mu idan mutum ya yi mafarki ko wane iri ne domin samun kwanciyar hankali da biyan bukata.”

(Insha ALLAHu za muji ci gaban bayanin a rubutu nagaba)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »