Bani Da Lafiya Kashi Na Daya

0 520

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

الحمد لله بسم الله والصلاة والسلام على رسول الله وعلى آله وصحبه أجمعين والتابعين لهم بإحسان إلى يوم الدين.

Wannan rubutu kamar yadda aka fara ganin takensa da suna : BA NI DA LAFIYA, wani sako ne da kuma fadakarwa ga marasa lafiya da masu bayar da magani cikin wani salo na labari da ke kunshe da fadakarwa, ilmantarwa da kuma wa’azantarwa cikin nishadi a bisa tsarin da shari’ah take maraba da shi.

Duba da yadda mabarnata suka shigo harkar bayar da magani gadan-gadan, da kuma yadda tsananin ciwo ke sanya wasu marasa lafiyar da iyayensu ko iyalansu zuwa wajan ko wanne irin mai magani da amsar duk maganin da sukaji labarinsa, ba tare da la’akari da Halarcinsa a shari’ar Allah ba, shi ne makasudin wannan rubutun domin mu gudu tare kuma mu tsira tare.

Ina kara rokon Allah subhanahu wata’ala mai kowa da komai, sarkin da ya halicci cututtuka kuma ya halicci maganinsu sai yabar ikon warkar da wanda yaso a hannunsa SHI kadai Sarki gwani mai cikakkiyar Hikima, da ya kiyayemin tunanina wajan tunato abinda ya yarda da shi da kaucewa abinda yake kyamarsa, kuma yayi riko da hannuwa na da alqalami na wajan rubuta abinda yadace da shari’aSA ba tare da na yi tsallen badake ba, ya yafe min tuntuben alqalami wanda na ana ba makawa sai anyi saboda hali na Dan’Adamtaka.

Wannan rubutun ba lallai ne yayi daidai da sauran rubutun labaran Hausa ba sak, saboda ƙarancin Hausa ta da kuma rashin kwarewa a fagen rubutun hausa da ka’idodinsa, sai dai jama’a su yi hakuri idan anga kuskure wajan rashin tsara rubutun labari yadda yakamata to ayimin afuwa da ma ba fage na bane, kawai bukata ta shi ne Sakon ya fita kuma a fahimcesa sannan ayi aiki da su Allah yasa mudace.

KAI TSAYE….

Tun Labeeba na da shekaru 4 zuwa 5 take fama da wani irin rashin lafiya mai fizgar tunani amma iyayenta basu kula ba, saboda gani suke yi ai ba wani abu bane.

Labeeba ta fara tasowa har ta girma ta kai minzalin da tafara jinin Al’ada, kawai sai rashin lafiyar yakara tsananta, duk alamomin da iyayenta ke gani a lokacin da take karama suka kara fitowa fili tayadda hankalin kowa yatashi….

(Insha ALLAHu za muhimmanci ci gaban a rubutu nagaba..)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.

Domin karin bayani:

WhatsApp
+2348031542026

Gmail:
rismawy86@gmail.com

Telegram Channel:
https://t.me/Rismawymedicine

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »