Ba Ni Da Lafiya Kashi Na Hudu

0 578

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Abu Labeeba: Yooo ke in banda abinki ba kya jin malamai suna cewa: Annabi ya ce: “Idan mutum ya yi mafarkin abinda yake kyama ( mara kyau) sai ya roki ALLAH ya tsare shi daga sharrinsa, kuma kar ya kuskura ya sanar da kowa mafarkin,

Kuma idan yayi mafarkin abinda yake so ( mai kyau) sai yayi Addu’ar Allah ya sada shi da Alkhairinsa kuma ya kare shi daga sharrin sa, kuma kar ya kuskura ya fadawa kowa sai wasu wadanda ya aminta da su ( su ma marasa yawa).”

“Tabbas kam da ana yin haka da gurbatattun malamai sun daina hallakar da mutane, da kowa ya rika samun nutsuwa saboda abu ne mai sauki wanda Addini ne ya koyar da hakan kuma kasamu biyan buƙatar ka. Allah yasa mudace.”

Ummu Labeeba tace kwarai kuwa Maigida, na fahimci wannan kuma na fadaka sosai da hakan, ALLAH ya shige mana gaba, Ameen.

Labeeba tana zaune ita kadai tasan abinda take ji a jikinta na lalurar da take fama da ita, batayi nauyin baki ba nan take ta bude baki tana cewa:

” Umma, Ni dai don ALLAH akaini wajan mai magani nasan abinda ke damuna ko ALLAH zai raba Ni da shi saboda wallahy lamarin nan yana matuƙar damun rayuwa ta.”

Abu Labeeba yace: Insha ALLAHu kuwa Labeeba ai shirin da muke yi kenan ma yanzu, bari dai na zagaya ( na shiga toilet) nadawo sai mu wuce ko !

Bayan wucewar Abu Labeeba kenan, sai ga wata makobciyarsu (mai suna SALAHA) nan ta yi sallama har ta samu wuri ta zauna, sai taga Labeeba dai ba yadda ta saba ganinta ba duk ta sauya, sai take tambaya tana cewa: Wai anya kuwa Labeeba kalau take?

Ummu Labeeba batayi wata-wata ba sai ta fara zayyana mata duk abinda ke faruwa da Labeeba, tana cewa: Wallahy abin nan ya ishe mu, kuma ga shi ita ba wai kyau ne ta rasa ba ko wani abinda ke sa a auri mace ba, amma kuma aure ya gagara duk kusan kawayenta sunyi aure sun barta, wannan abun na damuna sosai wallahy, Shi yasa za muje wajan wani mai magani.

Salaha: Ayyah ai kam da na nuna muku wata mai bayar da irin maganin nan, saboda ita yadda ma take bayar da maganinta abin ba a magana.

Ummu Labeeba ta gyara zama (alamun dai batun ya tsakuri zuciyarta) cikin mamaki sai tace: Ikon Allah kenan, ai dama kowa da irin baiwarsa, ita kuma ya take yin nata maganin ne?

Salaha: Ai in gaya miki kuna zuwa wajanta ba ma sai kun sanar da ita abinda yakawo ku ba za kuji ta fadi abinda ya kawo ku…

Ummu Labeeba jikinta yayi sanyi saboda ta san dai Abu Labeeba ko kadan bai kaunar batun irin masu maganin nan balle arika zuwa wuraren su, sai tace: Kuma kina ganin ba Bokanya bace matar kuwa?

Salaha: Wacce irin Bokanya kuma, ke dai ba dai diyarki ta samu lafiya ba ki huta da wahalar nan kawai a wuce wurin, shi yasa wallahy irin ku ke dadewa da ciwo a jikinsu saboda feleke da tsarin ku ya yi yawa.

“Duk tsananin zafin ciwo matukar kana so ka wanye lafiya da jikinka da imaninka kar mutum ya kuskura yakai kukansa wajan masu sanya rigar Allah suna kokarin tabbatar da abinda Allah ne kadai ke da hurumin haka, ko suyi yunkurin daqile abinda Allah ne kadai ke da ikon hakan, kuma hakan yana sanya ALLAH yayi fushi da mutum, ya nesanta shi da RahamarSA na har abada matukar bai tuba ba.”

Ummu Labeeba dai jikinta ya fara sanyi alamun shedan ya fara kwankwasa zuciyarta dangane da maganar Salaha, sai ta shiga saqe-saqe a zuciyarta tana zancen zuci ita kadai tana cewa:

“To, yanzu dai ga yarinyar nan da wannan ciwon sannan kuma ga shi Babanta ba son zuwa wuraren maganin nan yake ba ni kuma gaskiya abin yarinyar nan ya ishe ni, idan har mukace mu zura ido gsky fa akwai matsala, amma bari dai mugani…”

Salaha taga dai kamar Ummu Labeeba tana tunanin wani abu ne ( saboda ganinta da tayi ta yi jugumm), sai tace: Bari dai ni na koma gida, idan kika gama tunanin ko shawararar in har kuma son lafiyar diyarku na san za ku nemeni.

Salaha tana fita kenan, sai Labeeba ta matso kusa da Ummanta tana cewa: Umma, a islamiyyar mu fa ance mu guji zuwa irin wuraren magungunan nan saboda Bokaye ne kuma haramun ne zuwa wajen su, saboda suna damkawa wani mahaluki ne aikin da Allah ne kadai zai iya, gwara dai muje inda yadace kar muje mu afka ga halaka a karshe kuma ciwo ya dagule kuma ALLAH yayi fushi da mu.

Ummu Labeeba ta dallarawa Labeeba wata irin harara ta hankade ta can gefe tana cewa: Ke dilla can… Mara kan gado kawai, ke da ake nemarwa mafita, mu dai ba dai kisamu lafiya ba kawai mu huta, kinzo kina yi min wani wa’azi mara kunya kawai… Tashi ki bar nan wurin ko kuma na bibbige ki yanzun nan.

Labeeba ta fara zubar da hawaye sai ta tashi ta bar wurin cikin yanayi na rashin nutsuwa,

Jim kadan sai ga Abu Labeeba ya fito daga banɗakin yana cewa: Ina Labeeba din take ne, ku shirya mu wuce wajan mai maganin ko.

Ummu Labeeba tayi ajiyar zuciya tace: Hmmmm Abu Labeeba, don ALLAH zauna mu dan tattauna wata magana tukunna kafin mu tafi.

(Insha ALLAHu za miji abinda Ummu Labeeba da Abu Labeeba suka tattauna a rubutu nagaba.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »