Ba Ni Da Lafiya Kashi Na Biyar (5)

0 473

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Abu Labeeba yayi mamaki yana cewa: Na zauna fa kika ce?

Ummu Labeeba tace: Kwarai kuwa, abune mai muhimmanci ne ai wanda kuma duk ya shafe mu.

Bayan ya zauna ne sai Ummu Labeeba take ce masa: Yanzu makobciyar mu Salaha ta shigo ta tarar da halin da Labeeba ke ciki, kuma ga abinda ta ba mu shawara akai nan…

Bayan ta gama zayyana masa ne sai Abu Labeeba ya rike baki yana girgiza kai ( alamun dai abin ya bashi mamaki sosai) yana cewa: Inna lillahi wa inna ilaihi Raji’un…! Yanzu Ummu Labeeba don ALLAH meye amfanin zuwa irin wuraren nan neman magani bayan kinsan Addinin mu ya hana mu aikata hakan.

Ummu Labeeba : Yoo Abu Labeeba banda abinka ba dai daga anyi kuma an rabu da lalurar ba shikenan an huta, ai ba sake yi za ayi ba ko kuwa?

Abu Labeeba: Ai matsalar ba anan take ba, qaddara ma anyi din an samu lafiyar shin ya za muyi da babban laifin da muka aikata na zuwa wajan bokanya neman magani?

Ummu Labeeba: Hmmm Abu Labeeba kenan, kai wallahi matsalar ka kenan bini-bini wa’azi alhalin kuma Allah babu abinda ba ya iya yafewa.

Abu Labeeba: Eh na ji din, amma dai yafiyar yana yinta ne ga wanda yaga dama ko kuwa dole akeyi maSA ? To ni dai da in yarda mukai yarinyar nan wurin irin mutanen nan na gwmamace muyita zama a haka da ita har karshen rayuwar mu ko rayuwarta.

“Haka ake son Maigida ya kasance jajirtacce a gidansa, kuma yarika tabbatar da ana yin abinda Addini ke bukata a gidan ba wanda Addini ke Allah wadai ba, saboda gudun abinda ka iya zuwa yadawo kuma ya tseratar da kansa da iyalansa daga afkawa wutar jahannama.”

A lokacin dai Ummu Labeeb ranta idan ya yi dubu to ya baci, sai take cewa: Ni wallahy ina ganin ma kamar baka damu da matsalar yarinyar nan ba wallahy, saboda ka ki nema mata mafita saikace ba diyarka ba haba ..!

Abu Labeeba: Yoo Ummu Labeeba wacce mafita kuma kike so na kawo bayan na ce ku shirya muje wajan mai maganin da yadace da Shari’ar Muslunci don gudun kar mu afka ga halaka a karshe Allah yayi fushi da mu.

Nan dai Abu Labeeba ya Mike tsaye yace: Ina Labeeba din take ne ta fito muje wurin mai maganin ni da ita idan har ke ba zaki iya zuwa ba.

Haka kuwa akayi….Abu Labeeba suka fita shi da Labeeba, ita kuwa Ummu labeeba tayi kememe taki zuwa tayi zamanta a gida ko tace musu adawo lafiya batace ba.

Suna zuwa wurin wani mai magani sai suka tarar akwai jama’a sai Abu Labeeba ya nemi wuri ya zauna kusa da wani mutum ana ce masa (Abu Huda), itama Labeeba ta koma bangaren mata ta zauna.

Abu Labeeba yayi masa sallama sai ya amsa, sai suka zauna kusa da shi.

Jim kadan sai Abu Labeeba ya tambayi Abu Huda yace: Kaima maganin kazo karba ne haka?

Abu Huda: Eh wallahi, yarinya ta ce (Huda) ke fama da matsalar jinnu, sun hana ta aure duk wanda yazo sai dai kaga ya daina zuwa ba tare da wani dalili ba, itama kanta kuma rana fama da wasu matsaltsalun da mun kashe kudi a asibiti kamar me… abin ya ishe mu wallahi, sai muka ci karo da wasu rubututtuka da ke yawo a WhatsApp mai suna BANBANCI da kuma MAFITA , sai muka fahimci lallaikam yarinyar nan tana da jinnu a jikinta.

Abu Labeeba ya gyara zama yace: Subhanallah ! Aljanun suna tashi a jikinta ne ko kuwa ta yaya kai ka fahimci aljanu ne ke kawo irin haka?

Abu Huda: Ko kadan wallahi basu taba tashi ba, da yake ta tabayin aure ne a baya, amma auren ya bamu wahala kwarai da gaske a karshe dai auren rabuwa yayi, yanzu tana shekara ta 9 kenan da rabuwar aurenta kuma ba bu wani tsayayye har yanzu.

Sai alamomin nanne da muka gani a rubutun kuma naga duk tana fama da su, ga cututtuka daga wannan sai wannan har dai muka lura cewa lallaikam akwai wani abu da ke damun yarinyar nan.

Abu Labeeba: Allah Sarki, ka gani ko….ai shi yasa fa ba a bari kai yana kullewa a irin wannan lamarin.

Abu Huda: Ai kai dai bari dan uwa, mun sha wahala ba karama ba kam, amma yanzu Alhamdulillah yarinyar tana samun sauki kadan kadan da yake mun jima muna zuwa nan, yanzu ma wani auren za ta kara bayan Sallah Insha ALLAHu.

Abu Labeeba: Masha Allah, Allah yatabbatar da Alkhairi kuma yakawo mana na yan baya,, yanzu kai na ita yarinyar taka din take?

Abu Huda: Ga ta can a zaune kusa da wacce kukazo tare.

Abu Labeeba : Masha Allah, ka ga su ma na ga kamar suna tattaunawa tsakaninsu…

Huda ta cewa Labeeba bayan sun kammala gaisawa : Ke kuma me ke damunki ne naga Abbanki ya kawo ki nan?

Labeeba : Ai kema kinsan duk wanda kika gani anan to ba kalau ba.

Nan dai Labeeba tayi mata bayanin komai dangane da matsalar ta.

Huda tayi mamaki tace: Ikon Allah kenan, ashe dai duk matsalar mu kusan iri daya ce, sai dai ni ina ganin ma tawa ta fi ta ki matsalar, domin ni kinga har aure na tabayi amma suka hana ni zama har mijin yagaji ya sau ni.

Labeeba ta firgita sosai take cewa: Inna lillahi wa Inna ilaihi raji’un ! Na shiga uku ! Wai ashe lamarin nasu yana kaiwa har haka ne?

(Insha ALLAHu za muji bayani a rubutu nagaba)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »