Huda tayi murmushi tace: Hmm ai lamarin bayin Allahn nan sai Addu’a domin ni babu ma wanda zai ganni yace ina fama da su a zahiri saboda basu taba tashi a jikina ba, sai dai wasu cututtukan da nake fama da su.
Labeeba: Wallahy nima haka nake, basu taba tashi ba sai masifar ciwo kala kala daga wannan sai wannan.
Huda: Ai na dade ina neman magani sai daga baya naji labarin wannan malamin, amma kam a baya na je wuraren da imani na ma ya gushe, amma daga baya sai Allah yasa muka ankare.
Labeeba: Subhanallah ! Ai kinji irin matsalar ko, nima Wallahy saura kiris wata makobciyar mu ta ja ra’ayin Umma na muje wajan wata Bokanya.
Huda: Allah Sarki, ai kinji irinta ko, domin kuwa da kun kuskura kunje sai kun gane kuren ku, wallahy Ni wata kawata ce ma a school dinmu na bayyana mata ga abinda ke damuna, bayan ta ja ra’ayina sai kawai muka kama kafa muna zuwa wurin wasu bokaye.
Labeeba: Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un ! To ke bakisan boka bane a lokacin ?
Huda : Hmmm ina fa… Ai a lokacin idona ya rufe, na gaji da halin da nake ciki ne domin komai ma zan iya yi akan haka, saboda bukatata ni dai kawai na samu waraka, na manta cewa warakar a hannun Allah take.
Labeeba: To amma ya iyayenki suna sane da hakan kuwa?
Huda: Inaa… Ai ban ma bari sun sani ba, saboda na san Abban mu yana da tsanani sosai domin ba bari na zai yi naje ba.
“Sau da dama wasu yaran suna zuwa neman magani wuraren da shari’a ta haramta zuwa kuma su kasa sanar da iyayensu saboda bin shawarar kawaye ko kuma son zuciya, a karshe kuma ido ya raina fata saboda kwalliya ta kasa biyan kudin sabulu, gashi ba imani, ba nutsuwa kuma ba waraka, kuma ga fushin Allah da na iyayensu akansu. Allah ya kyauta.”
Labeeba: Amma kam kinyi kuskure gaskiya, ai iyaye su ne abokan shawara na farko da mutum zai fara fada musu matsalar sa ba kawaye ko wasu can dabam ba, saboda iyayenki ba za su iya kaiki inda suka san akwai cutuwa ba balle kuma duk abinda yasameki su ma suna jin kamar su ne ya samu har ma wani lokacin su fiki jin zafin ciwon.
Huda: Tabbas kuwa, ai ban lura da hakan ba sai daga baya, amma yanzu kinga alhamdulillah tare muke zuwa da Abbana.
Labeeba: Alhamdulillah Maasha ALLAH, ai kawaye wasunsu suna da matsala ba karama ba wallahy, saboda wasu hassada ce ta cika zuciyarsu, za kiga suna nuna miki kamar suna kaunarki nan kuwa ta ciki na ciki, sai dai kiga sun kai ki sun baro.
Huda tayi murmushi tace: Ke dai bari yar uwa, ai ni ne zan baki labarin nan kuwa, domin ita kawata din wacce ta nuna min zuwa gidan bokayen nan ashe dai idan munje itace ke zagayowa baya tana lalata abin kuma tayi ta yamadidi da ni a gari.
“Lallaikam ya kamata mutane su rika yin taka tsantsan wajan bayyana sirrinsu ga wasu da suke dauka a matsayin kawaye ko aminai, domin duk yadda kika dauke ta a Aminiya wacce ba zaki iya boye mata sirrinki ba to itama tana da wata Aminiya wacce ba za ta iya boye mata komai ba ciki kuma yadda sirrinki, saboda haka ayi hattara da wasu daga cikin kawaye.”
Sai Abu Huda yaji an kira shi ( layi ya zo kansu kenan), sai ya kira Huda suka shiga wajan Mai maganin tare.
Ba jimawa kuwa sai suka fito, aka kira su Abu Labeeba su ma suka shiga tare da Labeeba.
Sai mai maganin yace: Me ke tafe da ku?
Abu Labeeba yayi masa bayanin abinda ke faruwa da Labeeba tun farko.
Mai maganin yace: Subhanallah ! Ai irin wannan matsalar tun farko ne yake samun yara sakamakon sakacin da iyaye ke yi game da su.
Abu Labeeba yace : Subhanallah ! To Mallam kamar me da me kenan, saboda mu kiyaye a gaba?
Mai magani yaga bai kamata yayi maganar nan a gaban Labeeba ba saboda ita yarinya ce kuma su iyayenta ne, sai cewa yayi : Kafin nan dai bari mugama da ita yarinyar tukuna.
Mai magani yaci gaba da yiwa Labeeba nasiha kamar haka: Wato irin wannan matsalar tana bukatar tsarkin zuciya, mutum ya tsarkake zuciyarsa ta yadda zai san cewa babu wanda zai iya dora masa wannan lalurar sai ALLAH, kuma SHI kaɗai ne ke da ikon warkar da shi.
Kisani cewa: Yawaita ambaton Allah a ko da yaushe da kiyaye dokokinSA ba dare ba rana da karatun Alqur’ani da sauraronSA da kuma sanya sutura ta mutunci da kamewa da nutsuwa duk suna sanya shedanu nesantar mai wadan nan siffofin.
Saboda haka ki yawaita istigfari kuma ki tabbatar kin daina aikata abubuwan da ALLAH ba ya so ko da zuciyar ki tana so, kuma ki lizimci aikata abinda Allah ke so ko da zuciyarki ba ta so kuwa. Sannan ki kwantar da hankalinki za a hada miki mganin da za ki rabu da wannan matsalar da yardar Allah. Ta shi kije ki jira mu a waje.
Labeeba tace: Mallam Allah yasaka da Alkhairi kuma Insha ALLAHu zan kiyaye, Abba sai kun fito ina waje ina tsumayin ku.
Mai magani ya juyo wajan Abu Labeeba yana cewa: Ka ga na farko shi ne rashin yin Addu’ar da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya tarbiyyantar da mu yayin da ma’aurata za suyi saduwar aure da junansu.
Abu Labeeba: Lallaikam Mallam, gaskiya ana yin sakaci da dama a wannan fannin, domin da yawa ma ba iyawa sukayi ba balle su rika karantawa, waɗanda suka iya kuma ba kowa ne ke dabbaqa ta ba.
Mai magani: Kuma fa ba wani tsayi ne da ita ba, kawai mutum kafin ya sadu da iyalinsa sai yace:
Da Larabci
بسم الله، اللهم جنبنا الشيطان, وجنب الشيطان ما رزقتنا
Da Hausa:
“Bismillah, Allahumma jannabnash shaidãna, wa jannibish shaidãna mã razaqtanã.”
Kuma duk wanda ya karanta ta a lokacin da zai sadu da iyalinsa matuƙar a daren ko lokacin ( da ya karanta addu’ar) Allah ya azurta su da rabo, to shaidan ba zai taba iya cutar da wannan jaririnba a cikin ciki da kuma bayan haihuwarsa.
Abu Labeeba : Maasha ALLAH, ka ji ingantaccen riga-kafi nan, ka ji kau-da-bara na asali kuma tsaftatattace sannan ga sauki ba tsayi kuma ba wahalar karantawa.
“lallaikam wannan addu’ar da wasu ma’auratan suka kaurace karanta ta ne yasa komai ya dagule, yanzu yakamata dai kowanne magidanci ya haddace ta kuma yarika karanta ta a inda ake karantawa domin neman kariyar ALLAH wa kansa da iyalansa daga sharrin shedanun Mutane da na Aljanu.”
Mai magani: Kwarai kuwa, to ka ga mataki na farko kenan da ake iya baiwa yara kariya tun kafin ma a dau cikinsu daga sharrin shedanu .
Abu Labeeba: Lallaikam na fahimta kwarai da gaske, kuma ina godiya kwarai da gaske .
Mai magani: Sannan na gaba kuma idan mace tana da ciki sai kaga tana yin abubuwan da Addini ya haramta kuma takasa yin abinda Addini ya umarce ta da yi, ba ruwanta da yin Addu’ar Allah yakare mata abinda ke cikinta kuma ya sauke ta lafiya.
Mai Magani yaci gaba da cewa: Bayan nan kuma sai kaga da zarar an haifi jariri tun kafin ayi masa Addu’a, sai kaga uwa ko Uban ko ma wasu yan uwa suna daukar hoton jaririn suna yin posting a kafafen sada zumunta da nufin cewa wai sun samu karuwa a taya su da Addu’a.
Abu Labeeba: Subhanallah ! Wato Mallam yin hakan da matsala kenan?
Mai Magani: Yoo ai idan Addu’ar ce za a nema ba sai an dora hoton jaririn ba, saboda a cikin masu ganin hoton nan ba lallai ne iya masoyanku ne za su gani ba, domin a cikin kafafen sada zumuntar nan akwai makiyanku, akwai Shedanun Aljanu da na mutane kamar Mayu da wasu miyagu kuma duk sun gani, sai kaga ma har da su a yin comments akan hoton.
Abu Labeeba yayi jigumm ya kasa cewa komai…
Mai magani yaci gaba da cewa: Shin su wadan nan ka san irin hassadar da ke cikin zuciyarsu kuwa? Ai ingaya maka idan ka raba yawancin matsalar da yaran nan ke fuskanta a yanzu cikin kashi 10% to kashi 8% a ciki za kaga duk Kambun baka ne ko kambun ido ko kuma hassada ce ta shafe su.
(Insha ALLAHu za muji ci gaban lamarin a rubutu nagaba.)
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.
Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.
(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.
Domin Ƙarin Bayani Game Da Darrusan Marubucin.
+2348031542026
https://t.me/Rismawymedicine
rismawy86@gmail.com