It dai wannan runduna ta hudu mai ɗunbin albarka ta kasance ne a shekara ta shida da hijirar manzon ALLAH {saw}.
It dai wannan runduna ta hudu ta tafi a karkashin jagorancin Muhammadu Dan Aslamat, barade talatin ne suka fita wannan yaƙi ko wanensu yana kana abin hawansa suka je garin yan ƙabilar bakaru Ɗan kilabi a wani gari da ake cewa Bariyya.
Haka dai wadannan Sahabbai suka shiga wannan gari suka far musu da yaƙi a inda suka kashe mutum goma daga cikin wadannan kafirai ragowar kuwa suka cika rigarsu da iska.
Su kuma Sahabbai suka samu nasarar koro dabbobin su. Suna cikin hanyar su ta dawo wa ne suka hadu da wani kafiri mai suna Sumamatu ɗan Usalu yana daga cikin manyan yan ƙabilar bani Hanifah, anan ma Sahabbai suka cafke shi suka tafi da shi a mazaunin fursunan yaki ba tare da sun san koshi waye bah.
Koda suka je dashi wurin Manzon ALLAH {saw} koda Manzon ALLAH yagan shi nan take ya gano waye shi Manzon ALLAH {saw} ya bijirowa da wannan Sarki addinin Musulunci amma yaƙi karbar addinin Musulunci, amma duk da haka Manzon ALLAH {saw} yaci gaba da kyautata masa sannan yayi umarnin asake shi kuma asaki duk wani dan ƙabilar wannan mutum.
To a lokacin da wannan mutum yaga kyawawan dabi’un Manzon ALLAH {saw} daga karmci da mutunci irin na Shugaban mu Annabi Muhammadu {saw} nan take sai yadawo wurin Annabi ya mika wuya ya Musulunta ba tare da an tilasta masaba, harma yake cewa da Manzon ALLAH {saw} yana mai cewa:::
Ya Manzon ALLAH {saw} kasani cewa walhi kafin yau yau dinnan babu wani wanda nake gaba da shi sama da kai kuma babu fuskar da nake ƙyamar in gani kamar fuskarka to amma yau fuskarka tazama itace mafi soyyuwar fuskoki a gareni, kuma walhi adacan babu wani addini da nake mutukar kinsa a zuciya sama da addinika to amma yanzu wallahi addinika shine mafi soyyuwar addinai a gareni dukkansu kuma wallahi ada can babu wani gari da nake mutukar adawa da shi kamar garinka to amma wallahi a yanzu nafi sansa fiye da dukkan garuruwan duniya baki daya.
Manzon ALLAH {saw} yayi mutukar farin ciki da Musuluntar wannan babban mutum mai karmici da girma a cikin mutanan sa, saboda ta sanadiyar Musuluntar sa anasamu wasu da dama daga cikin mutanansa sun mika wuya sun karɓi addinin gaskiya.
A lokacin da wannan Sarki ya kama hanyarsa ta komawarsa gida sai ya yanke shawarar shiga Makka domin yayi umara don haka kawai yana shiga garin Makka da yake suma kafiran Makka sunyi mutukar saninsa domin a garinsu ne suke suyo duk wani abinci na alfarma, ko da ya shiga garin makka sai ya fiti fili ya nunawa kafiran Makka cewa shifa ya karbi Musulunci
To daga farko su waɗannan sun so su cutar dashi amma kuma sai suka tuna gudun mawar da garinsu yake basu na kayan masarufi don haka sai suka rabu dashi amma sai da ya rantse musu da Allah bazai sake sayar musu da komai daga garin su ba har sai sunyi imani da Shugaban halitta, tun daga ranar wannan Sarki ya yanke alakar cinikayya dasu, a sandiyyar wannan abu da yay musu sun shiga cikin matsala to anan ne sai Manzon ALLAH {saw} ya aikawa wannan mutum cewa yaci gaba da harkar kasuwanci dasu saboda karamci na Shugaban halitta.
Shi kuma sarki Sumamatu nan take ya karbi wannan umarnin Shugaban halitta Annabi Muhammadu {saw} ya dawo da harkar kasuwan ci da su.
Sarki Sumamatu ya taka rawar gani sosai a cikin addini musulunci musanman ma a lokacin wafatin Manzo {saw} a yayin da mutane da dama sukayi RIDDA harma suka bi Musailamatul Kazzabi .
Shi kuma sarki Sumamatu ya zare dantse yaci gaba da kiran mutane yana nuna musu cewa lallai duk wanda yayi RIDDA yabi Musailamatul Kazzabi to lallai wannan ya taɓe bashi da rabo a duniya da kuma lahira.
To daga nan ne mafi yawa daga cikin mutanansa suka dawo, yardar ALLAH ta tabbata ga wanna sarki jarumi wato Sumamatu.
Wannan shine ƙarshen runduna ta Hudu a saurare mu a shiri na gaba don kawo muku runduna ta biyar na wata azzalumai ƙabila mai cutar da musulmai.
[…] post Runduna Ta Hudu A Shekara Ta Shida Bayan Hijirar Manzo SAW. appeared first on Alummar […]