Runduna tarihi ne da muka binciko muku shi na yadda Sahabban Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama sukayi runduna runduna don yaƙar kafirai maƙiya Allah da Manzo (SAW).
A Cikin wanann rubutu zamu kawo muku rundunonin da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya haɗa har runduna Bakwai wa’yanda Sahabbai suka wakilta don yaƙa da kuma fatatakar arana.
RUNDUNA TA DAYA
Mai Karatu wannan itace ruduna ta farko wacce manzon ALLAH {SAW} ya shiryata kuma ya aikata domin suje su tarbi wata gayar ayarin KAFIRAN kurashawa da suka dawo daga garin sham daga cikin wayanan kafirai akwai Abu jahal tsinannen Ubangiji, su wadanan musulmai da Manzon ALLAH {SAW} ya tura zuwa wannan fafatawa musulmai su talatin ne (30) amma su kuwa arna su dari uku ne(300).
Shugaban wannan runduna ta musulmai shi ne sayyidina hamza dan abdulmutalabi.
Ita dai wannan tuta da manzon ALLAH (saw) ya bayar itace tuta ta farko da manzon ALLAH (saw) ya tura runduna don daukaka addinin allah wannan kuwa yafaru ne acikin watan azumi shekara ta daya bayan hijira.
Ita dai wannan tuta fara manzon ALLAH ya mikata ga sojojin musulinci a inda wani sahabi mai suna marsadu dan kanzi dan husaini ya karbi wannan tuta suk nausa suka tafi tare da umarnin manzon (saw).
A lokacin da wadannan bangarori biyu suka hadu suka daidaita domin fara yakar junan su kowanen su yayi sahu nan take sai ga wani mutum wada ake kira da suna majidiyu dan umar, yazo ya shiga tsakanin rundunar musulmai da ta kafirai shi wannan mutum yana da mutunci kuma mutum ne mai adalci wanda kafirai da musulmai suna ganin kimarsa, kuma bai zamo mai kar kata ga musulmai ko kafirai ba shi wannan mutum shi yay sulhu a wannan yaki yazama ba’a fafata ba .
Sayyidina hamza ya dawo tare da baradensa zuwa garin madina bayan hantar kafirai ta kada sun fara shiga taitayinsu kuma sun tsorata daga bin wannan hanya wacce suke bi don yin kasuwancinsu.
Mai karatu wannanitace runduna ta farko a cikin rundinonin musilunci kuma munji ba’a samu wannan fafatwa ba sai dai musulmai sun razana kafirai domin sun nuna musu cewa musilmai ba matsorata bane. Jarumai ne kuma sadaukai ne.
To amma a cikin watan shawwal ne kuma Manzon allah {saw} ya sake aika wata runduna a bias jagorancin Ubaidatu dan Harisdatu yana jagorantar sadukai tamanin suna haye da dawakai suka je suka tarbi kafirai dari biyu tutar muslinci tana hanun Masdahu dan Asasatu.
Musilmai sun hadu da kafirai a wani guri da ake cewa badanurabigu, shi gurin mil goma ne daga Duhfa zuwa abwa’I. to a Cikin wannan daji ne musilmai suka dingaiwa kafirai ruwan kibiya baji ba gani.
Duk da yake dai kafirai ne mafiya yawa amma duk da bala’I yay yawa duk sai suka gudu bayan sunga mutuwa amma duk da haka asami manya daga cikin kafirai sun musilinta, Aswadu da Utbatu. Haka kuma acikin wannan shekara ne allah yayiwa Usmana dan Mu’azanu rasuwa wanda shi wannan musilmi dan uwan manzon allah ne {saw} a bangaren shayarwa , wato sun sha nono daya da manzonallah {SAW}.
Kuma a cikin wannan shekara ne dai wani sahabi mai suna As’adu dan Zararata yayi wafati, shima wani sahabi mai suna Barar’u dan Ma’arur yayi wafati.
Haka dai acikin wannan shekara wani daga cikin manyan mushirikai suka mutu wato Walidu dan Mugira shima Asi dan Wa’ilu acikin wannan shekarar ya mutu . sai allah ya tserar da musilmai daga cikin wannan shakiyay biyu.
[…] post Runduna Ta Ɗaya Wanda Sayyiduna Hamza Ya Jagoranta. appeared first on Alummar […]