Ƙwakwa tanada amfani a dukkanin bangarorinta, kama daga kwallon kwakwan haryazuwa itaciyar kwakwar kai hattama bawon kwakwar yanada wani amfani nashi na daban, anayi amfani dashi wajen sarrafa wasu magunguna.
A wannan darasi zamuyi dubane muga tayanda ruwan kwakwa yakeda amfanuka iri-iri ga jikin dan Adam.
- Ruwan kwakwa ana iya shansa kuma ana iya zubashi asaman kai a cuda ilahirin kan, yanada amfani dayawa zamu kawo su nan gaba.
- Ruwan kwakwa yanada matukar tasiri wajen dawoda ruwan jiki,mai famada matsalar karancin ruwan jiki yayi amfani dashi.
- Yana da kyau mai motsa jiki ya shashi a yayin da yake motsa jiki Yana taimakawa.
- Yana taimakawa wajen hana samuwar cunkushewar koda wato (Kidney stones).
- Yanada sinadarai masu bawa ciki cikakken damar sarrafa abubuwan dake shiga dangane da abincin da ake ci yauda kullum (antioxidant)
- Shannsa yana taimakawa wajen hana kamuwa da ciwon suga.
- Yana kuma taimakawa masu matsalar hawan jini.
- Yana taimakawa wajen daidaita bugawar zuciya.
- Yana taimako wajen matsalar fitsari kowace iri.
Wanke Kai Da Ruwan Kwakwa.
- Yana taimakawa wajen magance matsalar ciwon kai.
- Yana yakar matsalar shaidanun aljanu idan ana wanke kai dashi.
- Yana sanya taushin gashi dakuma santsin gashi.
- Yana kawar da amosanin kai, yakarawa gashi karfi wajen hanashi karyewa, yasanya gashi ya kasance cikin danshi.
DAGA: Marhaba Islamic Medicine
Masha Allah