Yadda Zaki Kawar Da Bakin Guiwar Hannu da Yan Yatsun Hanunki .

0 824

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Ga masu bakin yan yatsu da kuma bakin gwaiwar Hannu musanman masu shafa mayukan hasken fata, wasu zakiga wadanan wurare yayi duhu sannan ragowar jikin nasu yayi haske, to insha Allahu da zarar kinyi wannan hadin hannuwanki zasu zama dai-dai.

ABUBUWAN DA ZAKI NEMA SUNE:

  • Cucumber.
  • Shinkafa.
  • Hydrogen.

YADDA ZAKI HADA WADANNAN KAYA

Dafarko zaki dau cucumber ki guda daya (1) saiki gogata a magogin goga kubewa, idan ta gogu saiki samu rariya mai kyau saiki tace ruwanta a kofi mai kyau saiki ajiye ruwan a gefe guda domin dashi zamuyi amfani a nan gaba.

Bakin gwaiwar hannu
yadda zaki goga cucumber dinki

Saiki Samu shinkafarki ki nikata tayi laushi sosai kamar fulawa itama ki ajiyeta a gefe guda.

Zaki hada ruwan cucumber da kika tace a baya saiki hadashi da nikakiyar shinkafrki wuri daya saiki kawo hydrogen din ki hada a ciki saiki juyasu sosai su juyu.

yadda zaki juya bayan kin hadasu wuri daya

Bayan kinjuya sun juyo saiki dinga diba kina gogawa a wadannan wurare maana gwaiwar hannu da yan yatsun hannuwanki bayan kin gam saiki barshi yadan samu kamar minti 2 saiki goge da tissue kokuma ki wanke.

Insha Allah cikin yan kwanki kalilan zakiga wurin yadawo kamar yadda ragowar jikinki yake.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »