Tarihin Zuwan Dariƙar Tijjaniyya Najeriya

0 9,682

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Zuwan Dariƙar Tijjaniya Nigeria

Tun a tarihin Shehu Ahmad Tijjani R.A. Shi mutumin Marocco ne, kuma wannan Dariƙa can ne masomintam bayan (Wafatin) Shehu Ahmad Tijjani R.A. Tijjaniyya ta cigaba da yaduwa a hannunsa Khalifa na farko zuwan Dariƙar tijjaniya Nigeria

Shehu Aliyu Harazumi Albarrada R.A. Wanda suka hadu da Shehu Ahmad Tijjani R.A. A (1777 AD/ 1155 AH) bayan dawowar Shehu Ahmad Tijjani R.A. Daga aikin hajji. Shi kuma Shehi Aliyi R.A. Da dan Dariƙar Hatutiyya ne, kafin haduwarsu da Shehu Ahmad Tijjani R.A.

Bayan Shehu Aliyu Harazumi R.A. Sai ‘Ya ‘Yan Shehu Ahmad Tijjani R.A. Biyi Shehu Muhammadul Kabir R.A. (D. 1827 AD/ 1205 AH) da Shehu Muhammadul Habib R.A. (D 1853/ 1231 A.H.) Bayansu Dariƙar Tijjaniyya ta shiga bangarorin Afrika ta yamma ta hannun Shehu Muhammadul Hafiz R.A. (D 1820 AD/ 1208AH) Almajirin Shehu Ahmad Tijjani R.A. Ne da ya yada Dariƙar Tijjaniyya a cikin danginsa da kabilarsa.

Hakan kuma ya zama sanadiyar yaduwarta a tsakanin Musulman Futa, ta hanyar Tafiye-Tafiyen Kasuwanci a cikin kasashen Sahara. A cikin Almajiransa Akwai Shehu Maulud Faal R.A. Da Shehu Abdulkarim Futa Jalo R.A. Wanda a sanadiyarsa Shehu Ummarul Futi R.A. “A WANI FADIN KUMA SHEHU UMMARUL FUTI R.A. YA KARBI Dariƙar TIJJANI NE DAGA SHEHU ALIYU HARAZUMI R.A”. Ya shiga Tijjaniyya, wanda ta hanyarsa ne, aka sami yaduwar ta a Afrika ta yamma.

Umar Bin Sa’idata, shi ne wanda ya yada Dariƙar Tijjaniyya a kudancin Sudan, ya kuma je kasashe da yawa a gabas ta tsakiya, ya je, Syria, Palastine, Misra,

Sai kuma Umar Bin Abubakar Falke (1893-1962 AD/ 1340 AH) Almajirin Shehu Abubakar Atiku R.A. Ne (Kano Nigeria) dan kasuwa ne da ya yi yawo sosai cikin Ghana da Sierra-Leone yana hada kasuwancinsa da yada Dariƙar Tijjaniyya, ya kuma je; Ilorin, Abeokuta da Lagos (Nigeria) Mukaddam Auwal na Oko-Awo, yana daga cikin Almajiransa.

Amma hakikanin lokacin da Dariƙar Tijjaniyya ta zo Najeriya yana da wuya don ana ma ganin tun zamanin Shehu Ahmad Tijjani R.A. Ta zo, saboda wasu daga cikin Malaman Madabo cikin birnin Kano ‘Yan Dariƙar Tijjaniyya ne tun kafin zuwan Shehu Ummarul Futi R.A. Wanda shi aka sani da wanda ya kawo Dariƙar Tijjaniyya Najeriya, su ka kuma sabunta Dariƙarsu a wajen su da mutanen Maiguduri da kukawa ta Jihar Barno lokacin da ya zo a (1832 AD/ 1210 AH).

Shehu Ummarul Futi R.A. Ya je Katsina, Zaria da Bauchi da ‘Yan Leman ya kuma je Sokoto a wajen (1832-1837AD) ya bar Sokoto bayan rasuwar Shehu Muhammad Bello R.A. Lokacin yana Sarkin Musulmai. Wannan shi ya sa ake kyautata zaton Muhammad Bello R.A. Ya shiga Dariƙar Tijjaniyya ne ta hannun Shehu Ummarul Futi R.A.

Abin da ya sanin hakikanin lokacin da Dariƙar Tijjaniyya ta zo Najeriya yana da wahala shi ne; Tun kafin zuwan ta akwai Dariƙun Sufaye kamar ƙadiriyya da Shazaliyya da wasu Musulmai suke yi musamman idan mutum ya duba tarihin daular Usmaniyya da rubuce-rubucen Shehu Usmanu Dan fodio R.A. Zai ga shi da dan uwansa, Shehu Abdullahi Gwandu R.A. ‘Yan Dariƙar ƙadiriyya ne, don haka lokacin da Dariƙar Tijjaniyya ta shigo Najeriya, bata zama wani sabin abu ba dangane da Musulunci da Musulmai, sai dai an ganta ne a matsayin sabuwar Dariƙa.

A wajen ƙarni na (w9) Dariƙar Tijjaniyya ta shiga kudancin Najeriya ta hannun Muhammad Wali, mutumin Ilorin, a kuma karshen sane aka ce Alfa Salih Abdulkadir (D. 1909 AD/ 1287 AH) ya kai Dariƙar Tijjaniyya Ibadan, lokacin da ya je Ilorin a wajen (1902).

Dariƙar Tijjaniyya ta samu a Ijebu+Ode (Ogun State) a ƙarni na Ashirin (20) ta hanyar ‘yan uwa kamar: Imam Hassan Amokeoja (D. 1920) da Alfa Alawaiye (D 1928).

Dariƙar Tijjjaniyya ta yadu ta hannun Sharif Ujudi da Sharif Alawi, wanda aka ce Shehu Muhammadu Salga R.A. Na Kano Ya karu da Sha’anin Dariƙa a wajensa. An kuma samu yaduwarta ta hanyar Mukaddamai da suke Wa’azi tare da yada Dariƙar Tijjaniyya, kamar: Sharif Zangina, Sharif Ahmad, Umar Falke, Sharif Ahmad Bin Salih, wanda ya maida Kano Masaukinsa a tafiye-tafiyen da ya yi, Ijebu-Ode, Kontagora, Ilorin, Ibadan da Lagos, yana koyar da Littafin: “MUNYATUL-MURID” Da “YAKUTATIL-FARIDAH”.

Rubuce-rubuce akan Dariƙar Tijjaniyya da ‘yan uwa suka yi musamman wadanda aka ambata sun kawo yaduwar Dariƙar Tijjaniyya tare da Shehu Ibrahim Niasse R.A. Da Almajiransa Kamar Su:

  1. Shehu Abdullahi R.A.
  2. Shehu Hassan Dim R.A.
  3. Shehu Mai~Hula R.A.
  4. Shehu Abubakar Atiki R.A.
  5. Shehu Sani Kafinga R.A.
  6. Shehu Tijjani Na ‘Yan Mota R.A.
  7. Shehu Yahuza Zaria R.A.
  8. Shehu Maddibo Jilani Yola R.A.

Da dai sauransu, insha Allahu zan kawo bayanan su a nan gaba kadan cikin garuruwan da Shehu Ibrahim Niasse R.A. Ya jaddada Dariƙar Tijjaniyya a lokacin zuwansa Kano (Nigeria).

Marubuci: Kamal Said Ibrahim

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »