SHIGARSU KASAR HAUSA
Wasu masu tarihi sun nuna wata kungiya ta Fulani sun fito daga kasar Sham wato daya daga cikin kasashen Larabawa har suka zo Futatoro suka shigo kasarnan a rarrabe.
Wani sashe na masu tarihi suna karfafa cewa, Fulani kabila daya ce, kuma daga tushe daya suke.
Sun shigo kasar Afirika ta yamma wato ta ketaren kasashen Larabawa daga wajen kasar Masar daidai gabar kogin Nilu, sai suka bazu a manyan kasashen Afirika irin su Libiya da Laberiya da Maroko da Aljeriya da Mali da Barkina-Faso har suka kwararo cikin Nijeriya ta Arewa.
A wata fadar kuma an ce, ‘Fulani sun fito daga kasar Sanagal.
Fulani da suka shigo kasar Hausa jinsi daya ne, sai dai sun kasu kashi biyu. Akwai Fulanin gida, wadanda ake wa lakabi da Fulanin soro sannan akwai masu yawon kiwo a daji masu zaga kasa-kasa gari-gari anai musu lakabi da Fulanin Daji (MAKIYAYA) .
FULANIN SORO: Galibinsu dogaye ne, wankan tarwada, kuma akan sami farare da bakake. Sannan masu kyawawan idanuwa ne da dogayen yatsu na kafa da na hannu. Yawancinsu makaranta Alkur’ani da littattafan tauhidi da sauran littattafan koyarwa na addinin Musulunci
Sana’arsu kiwo na cikin gida da noma. Halayensu kuwa sun hada da kunya da hakuri da yin liyafa ga baki da iya jagorancin jama’a. Fulanin gida ne kuma suka raya mulki na Musulunci a Arewacin Nijeriya.
FULANIN DAJI (MAKIYAYA) : Yawancinsu farare ne fat kuma kyawawan gaske kamar Larabawa. Wasu kuwa wankan tarwada ne, amma akan sami bakake kadan.
Suna da yawan gashi, mazansu da matansu. Fulanin daji ne suka fi wauta da jarunta, ga su da karfin hali da dauriya.
Sana’arsu kiwon dabbobi da saka irin ta kaba. Al’adarsu kuwa yawan tashi daga wannan wuri zuwa wancan suna tafe suna ta bushe-bushen sarewa, suna nema wa dabbobinsu abinci. Sukan zagaya kasashen da ake samun ciyawa a bakin kogi musamman lokacin rani. Basa son zama a cikin gari sai dole.
Sukan shiga gari ne kawai don sayen kayan masarufi.
ALIYU MUHAMAD FALGORE .JUGUDU.GIADE.BAUCHI.NIGERIA