Hanya Ta Biyu Wajen Kawar Da Amosanin Ka

0 2,545

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Kamar yadda muka fada a baya amosanin ka kanjawo wasu cutuka da dama daga kan har zuwa idonka kai harma zuwa kwakwalwarka. Don haka muka kuma binciko muku wata hanyar da zaa mangance wannan cuta ta amosanin ka. Wanda wannan ma idan anyita insha Allahu zaa rabu dashi cikin kan kanin lokaci.

ABUBUWAN BUKATA.

  • Lemon Tsami
  • Cucumber

  • Anti Dandruff shampoo

YADDA ZAA HADA MAGANIN.

Da farko idan kin samu cucumber taki mai kyau saiki bare bawanta sosai. Saiki yayanka ta kanana kanana saiki samu blender ko kuma wani dan karmin turmi mai tsafata sai a nika wannan cucumber din sosai bayan ta niku kota daku sai a samu abin matsewa kamar rariyar tace shayi kokuma na tace gasara. Sai a matse ruwan wannan cucumber a wan kofi mai kyau.

Yar uwa bayan kin matse ruwanta saiki samu lemon tsamin ki mai kyau shima saiki yankashi gida biyu saiki matse ruwan lemon tsamin a cikin ruwan cucumber din nan naki da kika tace a kofi. Saiki juya sosai ya juyi.

Bayan kin tabbatar ya hadu ya juyu saiki samu wani tsumma mai kyau kokuma audiga mai kyau saiki dinga tsomawa a wannan ruwan kina bude tsakan kanin gashin kanki kina shafawa a hankula har ki gama shafa ko ina a cikin kanki.

Bayan kin game shafe ko ina na cikin kan naki saiki kuma shafawa a gashin naki shima yasamu ko ina saiki barshi ya bushe na tsawon mintuna 30 ko 40. Sanan saiki kawo Anti dandruff Shampoo saiki wanke kanki dashi sosai.

ABIN LURA:

  • Amma kuma idan baki samu anti dandruff Shampoo ba zaki iya wankewa da wani kalar daban
  • Shi anti dandruff shampoo zakiyi amfani dashi ne saboda idan kin wanke dashi , gaahin kanki zaiyi kyau sosai sanan yayi kyalli ga kuma santsi.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »