YADDA ZAKU YI MAGANIN DUK WANI CIWAN IDO DAKE DAMUNKU TAYIN AMFANI DA NAMIJIN GORO
Wadan nan matakai na kasa da zan lissafo shine zakuyi amfani dashi wajen maganin duk wata cuta dake damun ku a cikin idonku ta hanyar amfani da namijin Goro.
Kutabbatar Kunnemi Wadannan Abubuwan Kamar Haka:
ABIN BUKATA:
- Namijin Goro mai Kyau.
- Karmar Roba mai Kyau kamar (robar maganin ciwon ido)
MATAKAN DA ZA’ABI WAJEN HADA MAGANIN
MATAKI NA DAYA:
Ku samu karamin roba mai murfi kuma mai tsafta, abu mafi sauki shine zaku iya samun robar maganin ciwon ido wanda akayi amfani dashi.
Idan robar maganin ciwon idon za’ayi amfani dashi to a tabbatar an wanke ko ina a ciki saboda a cire wannan ragowar rowa rowan maganin da ya rage a ciki.
MATAKI NA BIYU:
Sai a tafasa ruwa kadan kamar rabin kofi karami, A tabbatar cewa ruwan ya dahu sosai don ya kashe duk wasu kwayoyin cutar dake cikin ruwan.
MATAKI NA UKU:
Kudan saurara har sai wannan ruwa yayi sanyi sosai.
Amma kusani cewa ba lallai ne sai an dafa ruwan ba idan dai kunada ruwan roba ma’ana kamar irin su Faro ko makamatan ruwan roba wannan ba bukatar a dafa shi, tunda dama bukatar kawai yazama cewa ruwan babu wasu kwayoyin cuta (bakteriya) a ciki.
MATAKI NA HUDU:
Saiku zuba wannan ruwan a cikin roba mai murfin da kuka samo ko kuma (robar maganin ciwon idon da kuka wanke a MATAKI NA DAYA).
MATAKI NA BIYAR:
Saiku dauki namijin goranku mai kyau saiku dan rarabashi yada zai iya shiga cikin robarku dinnan wace kuka zuba ruwa aciki, bayan kun gama saiku sanya shi a cikin wanann roba.
MATAKI NA SHIDA:
Bayan kun gama zuba wannan namijin goro a cikin wannan roba da kuka zuba ruwanku, saiku daure bakin robar sosai, saiku samu wani daki saiku ajiyeta na tsawon kwanaki Ukku batare da wani ya taɓa shi ba.
MATAKI NA BAKWAI:
A rana ta uku da ajiye shi sai a dauko shi a girgiza sosai yadda ko ina zai juyo, sai a dinga digawa a idon dake ciwo kamar yadda ake diga maganin ciwon ido.
Zakuyi amfani dashi sau 2 ko sau 3 a rana ..
ABIN LURA A NAN
A rana ta farko da kuka diga wannan magani idanku zaiyi ja sosai, kada ku damu domin yana wanko da kuma tattaro duk wata datti dake cikin kwayar idonku.
Kuma bayan kwanaki biyu bazaku ga wannan jan da yakeba.
Sannan kuma kada ka rufe bakin robar da hanunka saboda gudun kada kwayar cuta ta shiga cikin maganinka.
BUGU DA KARI:
- Idan kana da GLAUCOMA, (wato wata cutace dake janyo makanta) za kuyi amfani dashi tsawon kwanaki 30-60 kuma zai tafi Insha Allah..
- Idan kuna da MYOPIA, (cutar da kansa bazakaga abu sosai ba idan yana nesa) kuyi amfani dashi tsawon kwanaki 21-30 kuma zaku gani a fili Insha Allah…
- Da kuma Duk wata matsalar da ta shafi ido wacce ta sanya maka saka tabarau zata warke cikin kwanaki 21-90 insha Allah.
Dole mai amfani da wannan maganin ya sabunta shi cikin kwanaki 21 na fara amfani da shi.
Ma’ana koda bai kareba cikin kwanaki ashirin da daya to dole ne ka zubar dashi kasake wani sabon hadin kamar na da.
Masha Allah, wassalamu-Alaikun Allah yabada lafiya daga shafinku har Kullum wato Alummar Hausa, shafi don kawo Muku Tarihin Kasar Hausa da kewaye tare da magungunan da Hausawan ke amfani dashi don maganin cututtuka.
Kuyi sharin zuwa manhajar #Facebook #Twitter ko kuma #Whatsapp don Alummar Hausa da wacce bata hausa ba ma su amfana.
Nagode da taimako
Salam Alaikum
Allah ya saka muku da babban rabo da wannan taimako da kuka kawo mana.
Inada tambaya
Namijin goron da zaayi amfani dashi shin guda nawa zaa saka a robar magani ?
Nagode
Guda Ɗaya ma Ya Isa Insha Allah
Ya zan yiwa murfin tunda samansa da kofa?
A’a bayan mai ƙofar akwai wanda yake rufe shi ai daga saman
Alh yasaka da alkhry
Allah yasaka da alkhairi
Salam alaikum
Inada tamnbaya shi goron mutum yana iya sanya rabi ne ko kuma duka dayan za’a sanya tunda naga ita robar maganin ciwon
ido karama ce
A’a Rabin ma ya isa, insha Allahu.
Jazakumullahu khairan. Amma Mallam Mai hakiya ko yanar Ido shima zai iya anfani da wannan?