Yadda Zaki Kara Yawan Gashin Kanki Tare Da Yin Baki

0 2,867

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

ABUBUWAN BUKATA.

 • Dankalin Turawa
 • Albasa
 • Blender
 • Kwai
 • Vitamin E
 • Shampoo

YADDA ZAKI HADA

Da farko zaki bare dankalin turawanki saiki yayyanka shi, sai albasarki itama ki yayyankata, saiki kawo blender dinki saiki nika albasar da kuma dankalin turawanki waje guda, idan ya nuku sosai saiki tace ta ki fitar da dusar saiki dau ruwan dashi zaayi amfani.

Bayan kitace saiki dauki ruwan saiki dauko kwanki saiki fasa a kai saiki juyashi sosai yada kwan zai hade sosai da wannan ruwan da kika tace,

Saikuma ki kawo Vitamin E dinki shima kisanya a ciki saiki kuma juyawa sosai yadda vitamin E din zai gauraye ko ina a ciki. Bayan kin tabbatar ya juyu saiki barshi har tsawon awa daya.

Shike nan ya hadu saiki shafe gashin naki sosai dashi. Bayan kin tabbatar kin shafe ko ina dashi saiki barshi har tsawon awa 1, saiki dauko man shampoo dinki ki wanke kan naki dashi. To insha Allahu kashin kanki zai koma kamar haka.

 1. Zaiyi Yawa
 2. Zaiyi Tsayi
 3. Zaiyi Laushi
 4. Zaiyi Kyalli
 5. Zaiyi Baki
Yadda zai koma idan yagama haduwa

Kuma bugu da kari zaki iya shafawa a hanayenki ko fuska shima yayi awa daya saiki wanke da sabul. Hakan zaisa fatarki tayi laushi da hasake

ABIN LURA:

 • Zaki iya yin haka a sati sau biyu kokuma yadda ya sauwaka insha Allah kafin wani lokaci zakiga canji.
 • Shi wannan vitamin E kina zuwa chemist zaki sameshi saiki siya.

Kinsan maza nason gashi ko to zakisha mamaki Allah yabada saaryi

Saura kuma in kingani ki boye ilimi kiki turwa wasu baruwa na nidai nayi kuma donku nayi.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »