Hanyar Dazaku bi Mafi Sauki Wajen Rage Tunbin Ku

2 1,599

Tunbi wasu lokutan kan bayyana ne bisa wasu abinci da kuke ci na yau da kullum, misalin irinsu shine wasu kafin karrin kumallon su (breakfast) kansha abu mai dauke da gas, shan abu mai gas da safe kansanya tunbi ya fito muku wanda idan kukaci gaba da haka zai haifar muku da dauwamamen tunbi.

Don haka idan kinsan kuna aikata haka to kudakatar ta hanyar samun abu mai dan dumi kusha kafin fara shan irin wadannan abubuwa, idan kuma bakwa shan wadancan abubuwan kawai yazo ne to sai ayi amfani da wannan maganin da zamu bayar.

ABUBUWAN BUKATA.

  • Albasa.
  • Lemon Tsami.
  • Ruwa.
  • Zuma.

YADDA ZAKU HADA MAGANIN.

Kidau albasarki mai kyau saiki bareta yadda yakamata saiki yayyanka ta kamar zakici salat, bayan kin gama yankawar saiki kawo blender dinki kizuba ta saiki kawo ruwa mai kyau ki zuba dan kadan saiki nika wannan albasa din sosai.

Idan kin tabbatar ta niku saiki debeta ki zuba a kofi mai kyau saiki kawo wannan lemon tsamin saiki matse a cikin wannan albasa da kika nika, saiki juya sosai.

Sai kuma ki kawo zuma dinki mai kyaun gaske wacce aka taceta saiki zuba a cikin kofin da wannan nikakiyar albasa take ciki saiki juya sosai.

Saiki kuma sanya ruwa kadan saiki kuma juyawa sosai, kitabbatar dukansu sun juyu.

Shikenan zaku dinga shansa Kullum kafin karin kumallo (Breakfast) da kuma kafin ku kwanta bacci. Insha Allahu ciki kankanin lokaci zakiga canji. Allah yatemaka.

Kamar yadda zaku dinga sha

Kuyi tambayar abinda baku ganeba sai munjiku.

Kuturawa Jama’a Don Suma Su Amfana

  1. Auwal Ahmad says

    Muna godiya allah yasaka da mafificin alkhairinsa amin, ga tambayata dana mene maganin amosanin kai wanda zakaga kan mutum yanayin wani abu kamar dusa dusa ka wani lokacin idonsa yana kaikayi inka mirtsika yayi ja, amma xuwa anjima zaidena. Nagode

    1. alummarhausa says

      Kadan bamu lokaci zamuyi darasin

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »