KARIN MAGANA GUDA DARI
1.
A daga sama! An yi wa wada kwace.
2.
A dauki kare ran farauta?
3.
A dauri kashi ko a bata igiya?
4.
A aiki kare ya aiki wutsiya?
5.
A amshi kadai ne, ba a ga mutuwa ba.
6.
A bakin tsoho ne, goro kan tsufa.
7.
A bakin wawa, akan ji magana.
8.
A bar dariyar mai noma, ko bai sayar ba, ya ci abinsa.
9.
A bar ganin allura kankanuwa,karfe ce.
10.
A bar kaza, cikin gashinta.
11.
A bari ya huce, shi kan kawo rabon wani.
12.
A ci a sha, a rage don gobe.
13.
A ci ba a sayar ba, kwai ya fi doki.
14.
A ci yau a ci gobe, shi ne ci.
15.
A cikin ido, ake tsawurya.
16.
A haifi da da samu, ya fi a mutu a bar masa gado.
17.
A ja mu a kai! An ba uwar makaho kashi.
18.
A kashe wuta, tun tana kankanuwa.
19.
A lallaba a kai ta, in ta fito muna so.
20.
A lokacin da mage na nan, bera ba ya wasa.
21.
A mari matacce, don mai rai ya ji tsoro.
22.
A nema a samu, arziki ne.
23.
A nuna wa na rigingine farin wata?
24.
A raba arne da makami.
25.
A rabe da alwalar kifi a ruwa?
26.
A rabe magirbin yakuwa, da na rama?
27.
A rabu a gana, arziki ne.
28.
A rama wa kura aniyarta.
29.
A rashin kira, karen bebe ya bata.
30.
A rashin kula, akan kade kudi.
31.
A rashin sani, bako ya sha ruwan wanka.
32.
A rika sara, ana duban bakin gatari.
33.
A sa a baka, ya fi a rataya.
34.
A san mutum, a san cinikinsa.
35.
A sayar a fadi, karin wayo.
36.
A shekara saran ruwa, sai tambatse.
37.
A so kare, har jelarsa.
38.
A so uwa, a so ‘ya’yanta.
39.
A tauna tsakuwa, don aya ta ji tsoro.
40.
A taya Allah kiwo, ya fi Allah na nan.
41.
A yi a gama, ya fi gobe a karasa.
42.
A yi abin da za a yi! Mahaukaci ya dauki rigar kurma.
43.
A yi maza, a fidda jaki daga duma.
44.
A yi wadda za a yi! Bera ya zubda garin kyanwa.
45.
A zaba a gasa, ta hana yaro suna.
46.
A zuba wa ungulu kwan zabuwa?
47.
Abin kwarai ya saba bacewa an dangana, ba takalmi ba.
48.
Abin al’ajabi! Ango ya kwanada kunzugu.
49.
Abin aljihu, na mai riga ne.
50.
Abin Allah! Budurwa da ciki; gwauro da yaye.
51.
Abin Allah! Budurwa da jika.
52.
Abin Allah, na Annabi ne.
53.
Abin aro, ba ya ado.
54.
Abin aro, bai rufe katara.
55.
Abin ba zai yiyu ba, auren mage da bera.
56.
Abin ba’a ne? An ce da kare mai sunan maza.
57.
Abin banza, hanci ba kafa.
58.
Abin biki, na biki ne.
59.
Abin cikin kwai, ya fi kwai dadi.
60.
Abin da aka gasa, shi ya ga wuta.
61.
Abin da aka shuka, shi yake tsira.
62.
Abin da Allah ya yi, Annabi sai ceto.
63.
Abin da babba ya gani daga zaune, yaro ko ya hau rimi ba zai linkaye shi ba.
64.
Abin da baki ya daura, hannubai iya kwancewa.
65.
Abin da dama ta jure, hagun ba ta jure ba.
66.
Abin da kamar wuya! Gurguwa da aure nesa.
67.
Abin da ke ga amarya, shi takan ba ango.
68.
Abin da ke gidan Sarki, akwai shi a kasuwa.68.
Abin da ke gidan Sarki, akwai shi a kasuwa.
69.
Abin da kunya, uwar ‘ya ta cinye suruki ran aure.
70.
Abin da mutum ya shuka, shizai girba.
71.
Abin da ruwan zafi ya dafa, in aka hakura ruwan sanyi ma ya dafa.
72.
Abin da wancan ya ce shi na ce! Kirarin mai tsoro.
73.
Abin da ya ba ka tsoro, wataran shi zai ba ka tausayi.
74.
Abin da ya ci Doma, ba ya barin Awai.
75.
Abin da ya ci ungulu, ba ya barin shaho.
76.
Abin da ya dami mutum, da shi yake mafarki.
77.
Abin da ya kewaye gida, gidan zai shiga.
78.
Abin da ya kora bera wuta, ya fi wutar zafi.
79.
Abin da ya taba hanci, ido saiya yi ruwa.
80.
Abin da ya zo, shi ake yayi.
81.
Abin daga Allah yake! Matar takaba ta yi ciki.
82.
Abin dariya! Yara sun tsinci hakori.
83.
Abin duniya mene ne? Kaza ta jawo muzuru kwanan gida.
84.
Abin duniya mene ne? Sarkinfawa da kyautar kaho.
85.
Abin fada, na mai baki ne.
86.
Abin majinyaci, na mai magani ne.
87.
Abin mamaki! Ciyawa da cin doki.
88.
Abin mamaki! Kare da tallan tsire.
89.
Abin mamaki! Kurege da fada wa zomo dadin kanzo.
90.
Abin mutum, abin wasansa.
91.
Abin na yi ne! An biya wa zawara hajji.
92.
Abin nema ya samu! Matar falke ta haifi jaki.
93.
Abin sai ido! Bebiya ta auri makadi.
94.
Abin shanya, ba a hana rana.
95.
Abin su na ‘yan dangi, bare ina ruwanka?
96.
Abin tsana! Amarya a kan kare.
97.
Abin tsoro! Kura a rumbu.
98.
Abin wani da wuya, nemi naka.
99.
Abin wani, bai yi wa wani magani.
100.
Abin ya zo daidai Mai ido daya ta leka buta.
i! Mai ido daya ya leka butabuta

Salon magana kuwa kamar a ce azanci kawai, akwai hikima a maganar amma ba ta zuwa da salo irin na Karin magana,kamar a Zaurance “Yazadazo ma’ana yazo kenan, a na sassarka wasu gabobi na kalma ne dan isar da sakon da salo, wani misalin shi ne sadannidu wato sannu kenan ko wani misalin ana iya daukar kalmar farko a maida ta karshe misali likaco wato cokali da dai sauransu.