TARIHIN MASARAUTAR KATSINA GIDAN KORAU A TAKAICE NA 1

0 2,479

Shi Gidan Korau da ke Katsina, Korau ɗin ne ya gina shi a wajen farko-farkon ƙarni na goma sha biyar. Korau an ce Musulmi ne wanda ake yi masa laƙabin Muhammadu Korau. Ya fito ne daga ƙabilar Wangarawa da ke rusasshiyar daular Mali. Shi Korau, tare da jama’arsa, sun mamaye ƙasar ‘Yandoto, wadda ke Zamfara, a farkon ƙarni na goma sha biyar (15). Daga nan kuma suka gangaro Katsina-Jigawa, suka yaƙi Sarkin Katsina da ke birnin Katsina mai suna Jibda Yaƙi Sanau.

Bayan cin nasara yaƙi, sai Korau ya ɗare karagar mulkin Katsina ya zama Sarkin Katsina na farko a tsatson Wangarawa. Kamar yadda bayani ya gabata cewa, Korau ne ya gina gidan Sarkin Katsina na yanzu da ke Cikin Gida, ya zauna a ciki har ƙarshen rayuwarsa. Haka ‘ya’ya da jikoki waɗanda suka yi Sarautar Katsina a daular Wangarawa, su ma a nan suka zauna tun daga shi Korau wanda ya yi zamani daga 1348-1398, har dai a ƙarshen mulkin Wangarawa a shekara ta 1807. An yi Sarakunan Katsina na Wangarawa waken guda ashirin da tara, kuma duk a nan Gidan Korau wanda ke Cikin Gida, suka yi Sarauta.

Muhimmai daga cikin waɗannan Sarakuna na Haɓe zuriyar Wangarawa, da suka yi mulkin Katsina, daga nan Gidan Korau da ke Cikin Gida, akwai Korau shi kansa. Akwai Ali Murabit, Ali Karyagiwa, Ibrahim Maje, Uban Yara, Janhazo, Gunawa Agwaragi, Sarki Gozo, Bawa Ɗangiwa, Maremawa, Magaji Halidu, da sauransu.

A lokacin mulkin Korau (1348-1398) aka gina gidan Sarkin Katsina da ke Cikin Gida, a lokacinsa ne aka tabbatar da kafuwar ƙasar Katsina wadda ta haɗa da Karofi, ‘Yanɗaka Durɓi, da sauran su, mai babban birni a Katsina, mai fada a Cikin Gida. Ali Murabit (1452-1475) da ya biyo baya, shi ya sa aka gina ganuwar Ƙofar Soro, wadda ta zagaye Gidan Korau, wadda aka yi wa ƙofofi guda biyu, Ƙofar Soro ta shiga fadar Sarki, da Ƙofar Bai, ta bayan gidan Sarki.

Tun daga zamanin Ali Murabit ne aka fara samun kafuwar Cikin Gida. Daga baya kuma, Ali Murabit, ya fara gina babbar ganuwar Katsina, wadda ta zagaye duk unguwannin da ke cikin birni Katsina. Amma ba a ƙarasa ginin ba sai zamanin Ibrahim Maje (1599-1613). Shi Ibrahim Maje baya ga ci gaba da ginin ganuwa, ya kuma ƙarfafa addinin Musulinci a ƙasar Katsina baki ɗayanta.

Shi kuma Ali Karyagiwa (1475-1525) wanda ya yi mulki kafin Ibrahim Maje, ya ƙara faɗaɗa ƙasar Katsina, inda aka kai yaƙi har Kuyambana da Birnin Gwari da Zamfara, don ƙara samun ƙasar mulki. Umurnin yin hakan ya fito ne daga fadar Cikin Gida. Kuma a zamanin Karyagiwa aka karɓi baƙuncin wani malami mai suna Muhammad Bin Ahmad Al-Tszakht, wanda aka fi sani da Ɗantakun. Shi Ɗantakun, ya zama babban alƙali a Katsina.

Lokacin mulkin Uban Yara da Janhazo (1708-1740) Katsina ta tsunduma cikin yaƙi da maƙwabtanta, musamman ma Gobir da Kano. A zamaninsa ne martabar malaman birnin Katsina, irin su Abu Abdullahi Bin Ghumehu Bin Nuh Al-Barnawi, Al-Katsinawi (Ɗanmasani), da kuma ɗayan malamin Muhammadu Bin Al-Sabbagh, Al-Katsinawi(Ɗanmasani), ta ɗaukaka, wato waɗannan malamai suka shahara a ko’ina a duniyar lokacinsu.

Shi kuma Gunawa Agwaragi (1779-1788), a lokacinsa aka dinga samun hamayyar gadon Sarauta tsakanin ‘ya’ya da jikoki na Sarakunan da suka gabata a nan Cikin Gida, wanda har abin ya kai ga yaƙin basasa.

Sarki Goza (1788-1802), shi kuma ya haɗu da fitinu na ‘yan Cikin Birnin Katsina da na ‘yan Cikin Gida. Haka aka yi ta yi har Bawa Ɗangiwa (1802-1804) ya zo, wanda shi ma ya ci gaba da fuskantar wannan fitina.

Su ‘yan Cikin Birni waɗanda ke yammacin Cikin Gida, ‘yan kasuwa ne attajirai da malamai masu ɗinbin ilmi da dukiya.

Su kuma ‘yan Cikin Gida, fadawan Sarki ne da barorinsa, bayinsa da barwansa da mayaƙansa. Wannan bambancin shi ya kawo kallon raini tsakani sassan biyu.

Baya ga wannan sai ga wata babbar sabuwar matsala ta fuskanci Bawa Ɗangiwa, mai fada a Cikin Gida. Matsalar kuwa ita ce ta jihadi, wanda ya ɓullo wa Katsina da masarautarta, a ƙarƙashin jagorancin Mallam Ummarum Dallaje da Malam Muhammadu Na’Alhaji da Mallam Ummaru Dumyawa.

Waɗannan Mujahidai sun karɓo tutar ƙaddamar da jihadi daga Sakkwato ga ƙasar Katsina baki ɗayanta, da masarautar Katsina ɗin da ke Cikin Gida.

An ci gaba da yin yaƙi tsakanin mayaƙan jama’a na masu jihadi da mayaƙan Sarakunan Katsina har Allah ya yi wa Ɗangiwa rasuwa. Wanda ya karɓi ragamar mulki da ci gaba da yaƙi, shi ne Muhammadu Maremawa

Muhammadu Maremawa (1804-1805), wanda a wata gwabzawar da aka yi a Iyatawa, aka kashe shi. Sai Magaji Halidu ya karɓi sarauta, aka ci gaba da yaƙi. A shekarar 1807, mayaƙan jama’a sun ci Katsina da yaƙi, inda shi Magaji Halidu (1805-1807) ya tsere zuwa Dankama daga can sai Damagaram.

Shi kuma Ummarun Dallaje (1807), wanda shi ne jagaban yaƙi ya shige gidan Sarautar gidan Korau da ke Cikin Gida, ya zama Sarkin Katsina na farko a daular Usman Ɗanfodiyo, a kuma zuriyar Fulani na Dallazawa.

Daga:

M.T.SAFANA ARCHIVES

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »