Na san mai karatu ya san abinda ake kira DINYA, wani irin yayan itace da yanzu sai a kauye a kan same shi.
Muna yara mun sha dinya kusan a kullun muka je jeji.
Amma ko mai karatu ya san dinya na daga cikin yayan itatuwan da ke da matukar amfani wajen yin magungunan cututtuka daban daban?
Dinyan kansa, da kwallonsa da kuma ganyensa dukkansu magunguna ne masu amfani a jikinmu.
Allah Ya mana arzikin magunguna, amma kash mun makale kan maganin bature ba tare da yin bincike da bunkasa namu ba da Allah Ya mana su iriiri a kewaye da mu.
Yanzu dai tun yaushe rabonka ko rabonki da shan dinya?
Ga kadan daga cikin maganin ko amfanin da dinya keyi a jikinmu.
KWALLON DINYA
CIWON SUGAR
A raba kwallon dinyan da tuwon kwallon Sai a shanya kwallon a rana har zuwa kwanaki uku zuwa hudu har sun bushe.
Idan sun bushe sai a fasa kwallon a dauko dan cikin kwalon wanda launinsa korekore ne.
Daga nan sai a farfasa wadannan yayan cikin kwallon a shanya su, na yan kwanaki a rana har su bushe.Sai kuma a nika su su zama gari.
Sai kuma a ajiye garin a kwalba a rufe sosai.
Za’a dauki ruwa kofi guda sannan a dauki cokalin tea na garin a zuba a cikin ruwan a gauraya a rinka sha da safe kafin a karya kumallo.
GANYEN DINYA
Ganyen dinya babban magani ne na attini wato kashin jini, Kuma yana iya hana sake kamuwa da cutar har na tsawon lokaci.
Ganyen dinya yana matukar maganin (kidney stones) wato dutsen koda.
A samu ganyen dinya kimanin nauyin gram 10 zuwa 15 a wanke sai a matse ruwansa a sanya kwayan bakin barkono guda uku a cikin ruwan a rinka sha sau biyu a rana na tsawon kwanaki za’a dace da yardan Allah.
Ganyen dinya na dauke da sinadarin da ke hana cutar daji/cancer a jikin mutum kuma yana hana ‘kari girma a jikin mutum.
Idan kana zazzabin da ya wuce kwanaki uku, sai ka jika ganyen kana sha domin yana rage zafin jiki.
Yana taimakawa wajen sa jini ya rinka gudana sosai a jikin mutum, wannan na taimakawa zuciya kwarai kuma ya magance kumburi a sakamakon rashin gudanar jini yadda ya kamata.
Idan kana da matsala a bakinka kamar wanda ke hanaka cin abinci ko zaizayewar fatan cikin baki, sai ka rinka wanke bakinka da ruwan ganyen dinya, yana warkar da shi cikin lokaci kankani da yardan Allah.
Haka yana kara maka karfin hakora.
Ganyen dinya na matukar maganin hawan jini.
mace mai matsalar rashin haihuwa saboda matsaloli a mahaifarta, tana iya matse ruwan ganyen ta sanya zuma a ciki tana sha.
A cewar masana da suka yi bincike na kasar India, sun tabbatar da cewar in aka hada ganyen dinya da yayan dinya fatar dinyan ana sha, yana maganin ciwon sugar kuma yana hana matsalar da ta kan faru na kashe karfin ido wa masu wannan ciwon na sugar.
Idan kina da kuraje a fuska, ana iya daka yaya/kwallon dinya a gauraya da madaran shanu sai a shafe fuska da shi kafin a kwanta sai a barshi sai da safe a wanke, yin hakan a kai a kai yana magance kurajen fuska.
Dinya yana da amfani wa masu karancin jini domin yana kunshe da sinadarin iron sosai da kuma vitamin C
Dinya da ya kai nauyin gram dari na dauke da sinadarin potassium da ya kai mg55 wannan adadin ya isa ya tiamaka wajen ciwon zuciya, hawan jini da stroke, in an jibinci shan dinya gwargwado ba a wuce gona da iri ba yana taimakawa wajen hana toshewar hanyoyin jini.
Kuma tana taimakawa wajen hana kamuwa da cutar hanta saboda yana kunshe da sinadarin da ake kira (POLYPHENOL)
KULAWA
- Masu ciki da masu shayarwa kada su yi amfani da dinya.
- Kada mutum ya sha dinya kafin da kuma bayan an masa tiyata domin yana rage karfin hawan jini.
- Wadannan mutane su kaurace wa shan dinya na makonni biyu akalla kafin da kuma bayan an musu aiki.
- A kaurace wa shan dinya in cikinka ba komai.
- A kaurace wa shan madara bayan an sha dinya.
- A kaurace wa shan dinya da yawan gaske a lokaci guda.domin zai haddasa matsala a makoshi/makogwaro da kirji kuma zai iya sa tari da kuma tara majina a kirji.
Masha Allah Atura a facebook ko WhatsApp