TARIHIN MARIGAYIYA AISHA LEMU

0 24,685

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

WANNAN SHINE TARIHIN MARIGAYIYA HAJIYA AISHA LEMU

 
An haifi Aisha Lemu a kasar Poole (Ingila), dake yankin  Dorset, a shekara ta 1940, inda ake kiranta da   Bridget Aisha Honey.

Lokacin  da tana yar  shekara goma sha uku (13), ta fara yin tunani na canza addini kuma ta fara nazarin sauran addinai, cikinsu har da addinin Buddha da na Hindu. 

Ta yi karatu a Jami’ar London  Makarantar koyan Al’adu da harsunan kasar sin da Africa wato school of oriental  and African studies (SOAS), a inda ta mai da hankalinta ga tarihin kasar Sin,  da al’adun su. 

Ta hadu da dalibai Musulmai a wannan Jami’a ta (SOAS)  waɗanda suka ba ta littattafan addinin musulunci ta ke karantawa,  kuma ta karbi Musulunci a Cibiyar Al’adu ta Musulunci a shekarata 1961, 

A shekarar farko ne a kartunta ta bada gudun mawa wajen samar da  kungiyar dalibai Musulmai a SOAS, a jami’ar ta London kuma itace sakatariyar kungiyar ta farko a makarantar. 

Bayan ta kammala karatun ta daga SOAS, Aisha ta tafi karatun digiri na biyu don koyan  turanci kuma a lokacin  ne ta hadu da mijinta, Sheikh Ahmed Lemu, wanda yake karatunsa a wata koleji a Jami’ar London kuma ya shiga cikin Ayyukan Musulunci a makarantun da suke yankin na london. 

Bayan da ta samu takardar shaidar gama digirinta na biyu a makarantar, ta koma Kano  a watan Agustan, a shekara ta 1966  ta fara koyarwa a Makarantar Nazarin Larabci a, inda Sheikh Ahmed Lemu ya yi aiki a matsayin shugaban makarantar. 

Sun yi aure da  Sheikh Ahmed Lemu a watan Afrilun shekara ta 1968,  Aisha ta zama matarsa ta biyu. 

Daga baya sai ta koma Sokoto don ta zama shugabar makarantar  Kwalejin ‘Yan mata ta gwamnati a sokoto.

Sheikh Ahmed Lemu shine babban kadi na kotun daukaka kara na shari’a a Nija lokacin da aka kafa ta a shekara ta 1976, Aisha kuma ita ce shugabar  babbar makarantar  malamai mata a Minna  har zuwa 1978. 

Ma’auratan biyu sun kafa Qungiyar Ilimin Musulunci wato Islamic Education Trust (IET) , wanda ke aiki a yanzu a cikin jihohin Najeriya da ke da ofisoshi da kuma ɗakin karatu,  da masu wallafawa, tare da makarantun primary da sakandare  da kuma makarantar manyan mata. 

Aisha Lemu na daya daga Cikin memba na Cibiyar Nazarin Musulunci, wanda Cibiyar Nazarin Ilimi ta Nijeriya ta kafa, wanda zai sake nazarin tsarin ilimin Musulunci na kasa a matakai daban-daban.

A shekara ta 1985, Aisha Lemu ta kafa kungiyar  mata Musulmai a Najeriya (FOMWAN) tare da sauran mata Musulmai,  kuma an zabe ta a matsayin shugabar musulmai mata ta kasa ta farko, kuma tayi shekaru hudu. 

Ta wallafa littafai da dama a fannin addinin Musulunci da ilimi wadanda aka rika amfani da su a makarantun sakandare na Najeriya. 

Aisha Lemu ta rasu a ranar Asabar 5, ga watan  Janairu 2019 a Minna ta jihar Neja a Nigeria tana da shekaru 79 a duniya.  

      Allah Yay rahama a gareta kuma Ya ba ta Aljanna madawamiya muma idan tamu tazo Allah yasa mucika da imani Amin. 

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »